Yanzu Yanzu: Ministan Buhari ya dakatar da shugabar REA

Yanzu Yanzu: Ministan Buhari ya dakatar da shugabar REA

- Ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman ya dakatar da Manajan Darakta ta hukumar , Rural Electrification Agency (REA), Ms Damilola Ogunbiyi

- Dakatarwar zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba kuma zai cigaba har sai baba ya gani

- Ministan ya kuma yi umurnin binciken gaggawa cikin ayyukan hukumar domin kawo sauyi a tsarin aikinta

Ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman ya dakatar da Manajan Darakta ta hukumar , Rural Electrification Agency (REA), Ms Damilola Ogunbiyi har sai baba ya gani.

Dakatarwar zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba, cewar mai bashi shawara na musamman, Mista Aaron Artimas, a wani jawabi a ranar Talata, 24 ga watan Disamba.

“Biyo bayan wasu karya dokoki a hukumar Rural Electrification Agency (REA), ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman ya umurci Manajan Darakta na hukumar, Ms Damilola Ogunbiyi da ta tafi hutun sai baba ya gani ba tare da bata lokaci ba.

“Ms Ogunbiyi za ta mika shugabanci ga jami’i mafi girma a hukumar.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta yi wa Kiristoci sha tara ta arziki domin bikin Kirsimeti

“Haka zalika, ministan ya yi umurnin binciken gaggawa cikin ayyukan hukumar domin kawo sauyi a tsarin aikinta.”

A wani labari na daban, mun ji cewa a ranar Litinin, 23 ga Watan Disamba, 2019, gwamnatin tarayya ta bakin Ministar kasuwanci da hada-hada, ta fito ta na cewa babu maganar ranar bude iyakokin kasa tukuna.

A watannin baya ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta garkame iyakokin kasa a sakamakon yawon fasa kauri da shigo da kaya da ake yi cikin Najeriya ta kasa.

Karamar Ministar kasuwancin Najeriya, Mariam Katagum ta fadawa ‘Yan jarida cewa gwamnatin tarayya ba ta fitar da matsaya a game da lokacin da za a bude iyakokin kasar ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel