Kuma dai: Babu tabbacin Najeriya za ta bude iyakokinta a farkon 2020

Kuma dai: Babu tabbacin Najeriya za ta bude iyakokinta a farkon 2020

A Ranar Litinin, 23 ga Watan Disamba, 2019, gwamnatin tarayya ta bakin Ministar kasuwanci da hada-hada, ta fito ta na cewa babu maganar ranar bude iyakokin kasa tukuna.

A watannin baya ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta garkame iyakokin kasa a sakamakon yawon fasa kauri da shigo da kaya da ake yi cikin Najeriya ta kasa.

A wani jawabi da gwamnatin Najeriya ta yi a baya, ta nuna alamun cewa za ta iya bude iyakokin kasar a Watan Junairun 2020. Yanzu gwamnatin kasar ta fito ta nuna ba haka ba.

Karamar Ministar kasuwancin Najeriya, Mariam Katagum ta fadawa ‘Yan jarida cewa gwamnatin tarayya ba ta fitar da matsaya a game da lokacin da za a bude iyakokin kasar ba.

Hajiya Mariam Katagum ta ce sai da Najeriya ta yi wasu zama masu muhimmanci da kasashen Benin da Nijar da ke makwabtka da ita domin ganin yadda za a bude iyakokin.

KU KARANTA: An bayyana wadanda ke hura wutan rikicin Jihar Kaduna

“Mun yi zama da Mawakbtan mu uku, kuma mun yarda tare za a kafa Dakaru mai dauke da Ma’aikatan Kwastam da Jami’an tsaro da za su tabbatar an bi dokokin ECOWAS.”

Ta ce: “Kwamitin ya zauna a Ranar 25 ga Watan Nuwamba, sai lokacin da kwamitin ya tabbatar cewa kasashen za su bi ka’idar ECOWAS, sannan za mu ce a sake bude iyakokin.”

Bayan wannan jawabi da Ministar ta yi, binciken da Jaridar Daily Trust ta yi, ya nuna cewa kawo yanzu ba a kafa wasu Dakaru da za su fara wannan aiki da ake magana ba.

Da farko dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za a bude iyakokin a watan gobe, daga baya ya lashe amansa, ya ce za a cigaba da garkamewar har sai an ga canji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel