Aisha Buhari ta yi wa Kiristoci sha tara ta arziki domin bikin Kirsimeti

Aisha Buhari ta yi wa Kiristoci sha tara ta arziki domin bikin Kirsimeti

- Hajiya Aisha, Uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da tallafin kayayyakin abinci ga kiristoci a cocin Our Lady Queen of Pro Cathedral Catholic Church of Nigeria, a ke Abuja

- Hakan na daga cikin shirin uwargidar shugaban kasar na tallafa wa gajiyayyu a fadin kasar

- Jigon cocin, John Jimoh wanda ya karbi kayayyakin a madadin cocin ya mika godiya ga uwargidar Shugaban kasar a kan wannan karamci nata

Uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta bayar da tallafin kayayyakin abinci ga iyalan Kirista a cocin Our Lady Queen of Pro Cathedral Catholic Church of Nigeria, Abuja.

Wole Aboderin, mai ba uwargidar Shugaban kasar shawara na musamman a kan harkokin tallafi, wanda ya gabatar da kayayyakin a madadinta, ya ce wannan karamcin ya fito ne daga zuciyar Aisha na son taimaka wa marasa karfi a kasar.

“Kirsimeti ya kasance lokaci na nuna wa juna so da kauna saboda ya kasance abun alkhairi ga mutane.

"Yayinda muke bikin, mu yi kokarin wanzar da farin cikinmu zuwa ga talakawa a gajiyayyu. Ina yi muku murnar bikin kirsimeti da sabuwar shekara mai albarka."

John Jimoh, jigon cocin wanda ya karbi kayayyakin a madadin cocin ya mika godiya ga uwargidar Shugaban kasar a kan wannan karamci nata.

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro masu ritaya ne ke rura wutar rikici a Kudancin Kaduna – Rundunar soji

Ya yaba mata akan cigaba a tallafawa gajiyayyu a kasar.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa za a yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin gajiyayyun cocin su ci moriyar shirin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel