Babbar magana: 'Yan bindiga sun sace matar sarki, 'ya'yansa mata biyu da direbansa

Babbar magana: 'Yan bindiga sun sace matar sarki, 'ya'yansa mata biyu da direbansa

- Wasu 'yan bindiga da ba san ko su waye ba sun sace matar wani basarake da 'ya'yan sa biyu

- Masu garkuwa da mutanen sun kira basaraken tare da bukatar miliyan 10 a matsayin kudin fansa

- Basaraken ya bukaci jami'an 'yan sanda da su taimaka wajen ceton iyalansa dake cikin hatsari

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace matar wani basarake mai suna Oba Rufus Olugboyega Akinrinmade, wanda shi ne Orunja na Odigbo dake ke karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.

Masu garkuwa da mutanen sun hada da 'ya'ya mata biyu na basaraken masu suna Mercy da Precious, har da direbansu.

DUBA WANNAN: Lamborghini da $5m: An cafke dan shugaban wata cibiyar tarayya a Dubai

Matar basaraken mai suna Regina Akinrinmade, 'ya'yan ta biyu da direbansu sun shiga hannun masu garkuwa da mutanen ne a ranar Asabar. An kama su ne a yayin da suke kan hanyar Oba Akoko ta Akungba Akoko don ziyarar daya daga cikin dan basaraken da ke karatu a jami'ar Adekunle Ajasin da ke jihar.

Oba Rufus Olugboyega Akinrinmade ya bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun tuntubeshi tare da bukatar kudin fansa har naira miliyan goma.

Basaraken ya bayyyana cewa, tuni ya garzaya gaban 'yan sanda don kai rahoton abinda ya faru. Ya kara da kira ga hukumar 'yan sandan da su tsananta bincike don samo masa iyalansa da ke cikin hatsari

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel