A ranar bikin zagayowar haihuwarta: Budurwa ta diro daga bene, ta rasa ranta

A ranar bikin zagayowar haihuwarta: Budurwa ta diro daga bene, ta rasa ranta

Jami'an 'yan sanda da jami'an ceto sun samu kiran gaggawa ne a bene mai hawa 38 da ke otal din Jomtien, Pattaya dake kasar Thailand a daren Lahadi. Hakan ya faru ne bayan da wata budurwa 'yar kasar Thailand ta diro daga hawa na 22 na benen otal din.

Wacce abun ya faru da ita mai suna Suthirak S.ta fado daga bene hawa na 22, kuma ta bige da bishiya kafin ta iso kasa. Ta samu munanan raunika wadanda suka yi sanadin mutuwarta.

A ranar bikin zagayowar haihuwarta: Budurwa ta diro daga bene, ta rasa ranta

Budurwa ta fado daga bene mai hawa 22 bayan samun sabani da saurayinta
Source: Facebook

Bayan tsananin bincike da jami'an suka gudanar, an gano cewa babu wata alama ta fada ko fafutukar ceton rai a daki mai lamba 2220, inda budurwar ta kama.

Kawun mamaciyar mai suna Bunpherm mai shekaru 43 ya ce, 'yan uwa da abokan arziki sun taru a garin ne don murnar zagayowar haihuwarta.

A ranar bikin zagayowar haihuwarta: Budurwa ta diro daga bene, ta rasa ranta

A ranar zagayowar haihuwarta, ta kashe kanta
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ayyiriri: Jaruma Halima Atete ta kusa zama amarya

A yayin da suke wajen cin abinci, Suthirak da saurayinta dan kasar Japan sun fara mummunan fada bayan da ta yi ikirarin cewa yana hirar da wata ta waya a yayin da yake liyafar zagayowar ranar haihuwarta.

A ranar bikin zagayowar haihuwarta: Budurwa ta diro daga bene, ta rasa ranta

Benen da budurwar ta fado
Source: Twitter

A can otal din, ta garkamesa a wani dakin. Ya buga kofar da duk karfinsa da bukatar su sasanta tsakaninsu.

Bayan nan ne aka hanzarta zuwa saman tare da sanar dashi cewa wata ta fado daga benen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel