Gwamnatin Ganduje ta garkame wani babban banki saboda bashin N423m

Gwamnatin Ganduje ta garkame wani babban banki saboda bashin N423m

Gwamnatin jahar Kano ta garkame bankunan Zenith Bank guda uku dake jahar Kano saboda nokewa wajen biyan harajin kudaden shiga da suka kai zambar kudi naira miliyan 423.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito hukumar tattara haraji ta jahar Kano ce ta gudanar da wannan aikin garkame bankunan dake kan hanyar Murtala Muhammad, Bello road da kuma titin gidan Zoo.

KU KARANTA: Hukumar Immigration ta gina sabon cibiyarta a kan N145m a mahaifar Buhari

Shugaban hukumar, Alhaji Sani Abdulqadir Dambo ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace tun shekarar 2014/2015 suke bin bankin bashin kudaden harajin, inda yace bankin ta saba sashi na 104 na kundin dokokin harajin kudaden shiga na shekarar 2011.

“Bayan mun tabbatar da adadin bashin da ake binsu, sai muka aika musu da takarda domin su biya wadannan kudade, kuma suka amsa takardar cikin lokacin daya dace, amma basu kudin duka ba, saboda a cewarsu suna da ja game da lissafinmu.

“Sai dai da muka zauna muka duba amsar da suka bamu, bamu gamsu da ita ba, saboda ba su tabbataccen hujja, don haka muka sake sanar dasu matsayinmu na lallai sai sun biya wadannan adadin kudi, amma har yau basu bamu martani ba.”Inji shi.

Alhaji Dambo yace wannan dalili ya sa suka mika kukansu ga Alkalin Alkalan jahar Kano, wanda ya mika maganan ga wani babban Allkali babbar kotun jahar Kano, mai sharia Ibrahim Umar domin ya yi nazari a kai, daga karshe Alkalin ya bayar da umarnin garkame bankunan.

Alhaji Dambo yace a yanzu zabi biyu ne ya rage ma bankin, kodai ta daukaka kara ko kuma ta biyan cikon bashin kudin harajin da gwamnatin jahar Kano take bin ta.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shirin kawo sasanci tare da sulhunta tsakanin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje tare da mai martaba Sarkin, Muhammadu Sunusi II.

Takun saka tsakanin gwamnan da Sarkin ya zurfafa ne tun bayan da gwamnan ya kirkiri sabbin masarautu guda hudu, kuma ya daga likafarsu zuwa masu daraja ta daya, daidai da na Sarki Sunusi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel