Jami’an tsaro masu ritaya ne ke rura wutar rikici a Kudancin Kaduna – Rundunar soji

Jami’an tsaro masu ritaya ne ke rura wutar rikici a Kudancin Kaduna – Rundunar soji

Kwamandan sojoji na Operation Safe Haven, Manjo Janar Augustine Agundu ya bukaci manoma da makiyaya a yankin kudancin Kaduna da su ajiye makaman da suka mallaka ba bisa ka’ida ba ko kuma su fuskanci barazanar kamu.

Ya kuma yi zargi wasu jami’an tsaro masu ritaya daga kudancin Kaduna da alhakin rura wutar rikici a yankin amma ya bayar da tabbacin cewa kwanan nan za a kama su.

Kwamandan, wanda ya bayyana hakan a Kafanchan a ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, a lokacin taron gwamnatin jihar Kaduna da Operation Safe Haven na hedkwatar tsaro da kuma masu ruwa da tsaki a kudancin Kaduna, ya ce ya zama dole makiyaya da manoma su dakatar da tsohuwar al’adarsu na daukar doka a hannayensu.

Manjo Janar Agundu, wanda ya yi magana sosai akan dalilin ya sa ya zama dole mutanen Kaduna su zauna lafiya da junansu, ya bukaci mazauna yankin da su san junansu sannan su kawo rahoton yan ta’adda a yankinsu zuwa ga hukumomin tsaro domin daukar mataki kan lokaci.

KU KARANTA KUMA: Kurunkus: Buhari ya yi karin haske a kan batun tazarcensa

Kwamandan wanda ya fara ziyartar shugaban Kagoro da Sarkin Jama’a a fadarsu, ya yi kira ga mazauna yankunan su kasance masu hakuri a tsakaninsu sannan ya gargadi masu tayar da zaune tsaye da su bar kudancin Kaduna ko kuma su fuskanci hukuncin doka.

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu gagararraun masu fasa kauri guda shida sun fada komar jami’an hukumar kwastam reshen jahar Katsina a kan wasu kayayyaki da suka shigo dasu ba tare da biyan harajin shigo da kayan ba daya kai naira miliyan 108.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwanturolan hukumar kwastam na jahar Katsina, Kiriwa Abdullahi ne ya bayyana haka yayin da bayyana kayayyakin ga manema labaru, inda yace an shigo da kayan ne a cikin motoci 73 da manyan tireloli 4.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel