Hukumar kwastam ta yi ram da kasurguman masu fasa kauri 6 a jahar Katsina

Hukumar kwastam ta yi ram da kasurguman masu fasa kauri 6 a jahar Katsina

Wasu gagararraun masu fasa kauri guda shida sun fada komar jami’an hukumar kwastam reshen jahar Katsina a kan wasu kayayyaki da suka shigo dasu ba tare da biyan harajin shigo da kayan ba daya kai naira miliyan 108.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwanturolan hukumar kwastam na jahar Katsina, Kiriwa Abdullahi ne ya bayyana haka yayin da bayyana kayayyakin ga manema labaru, inda yace an shigo da kayan ne a cikin motoci 73 da manyan tireloli 4.

KU KARANTA: Siyasa mugun wasa: An cigaba da tone tonen asiri tsakanin manyan gwamnanonin PDP 2

Daga cikin kayan akwai; buhunan shinkafar kasar waje 1,632, jarkan man gyada 440, dilan gwanjo guda 9, katan 283 na taliya, buhuna siga guda 81, kwali 26 na batir da kuma kwalaye 28 na taliyar macaroni.

Kwanturolan ya kara da cewa manyan tirelolin guda hudu na dauke ne da fatu, kanwa, batiran mota da kuma wata dake dauke da lita 50,000 na man gas. Daga karshe kuma ya karkare da cewa zasu gurfanar da mutanen gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

A wani labarin kuma, hukumar kula da shige da fice, watau Immigration, ta kaddamar da wani katafaren sabon sansaninta da ta gina a garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake jahar Katsina.

Kwanturolan hukumar na kasa, Mohammed Babandede ne ya jagoranci kaddamar da sansanin, inda yace sun gina sansanin ne domin yaki da ayyukan yan bindiga, masu safarar mutane da kuma shigowar bakin haure cikin Najeriya.

Babandede ya kara da cewa a baya jami’an hukumar dake aiki a kan iyakokin Najeriya basu da wata sansani ko cibiya da zasu dinga taruwa suna tsara yanayin aikinsu, wannan ma yana daga cikin dalilan da yasa hukumar ta gina wannan sabon sansani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel