Jam’iyyar PDP ta fara shirin sulhunta rigimar Gwamna Wike da Dickson - Ologbondiyan

Jam’iyyar PDP ta fara shirin sulhunta rigimar Gwamna Wike da Dickson - Ologbondiyan

Majalisar NWC ta jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ta fara kokarin kawo karshen rikicin da gwamnoninta Seriake Dickson na jihar Bayelsa da Nyesom Wike su ke yi.

Wadannan gwamnoni na Kudu maso Kudancin kasar sun samu kansu cikin sabani ne a dalilin rikicin da ake yi a kan rijiyoyin man Neja-Delta da kuma banbancin siyasa.

A wani jawabi da PDP ta fitar Ranar Litinin, 23 ga Watan Disamba, 2019, jam’iyyar ta bayyana cewa ta lura da duk matsalolin, kuma za ta shawo kansu cikin ruwan sanyi.

Jam’iyyar hamayyar ta yi wannan jawabi ne ta bakin Sakatarenta na yada labarai na kasa, Kola Ologbondiyan. A cewarsa, kishin jihohinsu ne ya kawo wannan sabanin.

“Shugabannin PDP su na kira ga Gwamnoni Wike da Dickson, a natsayinsu na Jagorori kuma manyan masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyarmu, su ajiye kayan fadansu…”

KU KARANTA: Gwamnan Ribas ya yi kaca-kaca da Seriake Dickson a sabon rikicin PDP

Jam’iyyar PDP ta fara shirin sulhunta rigimar Gwamna Wike da Dickson - Ologbondiyan

Kola Ologbondiyan ya ce ana kokarin sasanta Wike da Dickson
Source: Facebook

“A yayin da shugabannin PDP su ke sulhunta matslaar. Mu na kira ga Magoya bayanmu, musamman na Ribas da Bayelsa su kwantar da hankalinsu, su hada-kai…”

Kola Ologbondiyan ya cigaba da cewa yanzu haka an kama hanyar sasanta rikicin. “PDP ta na kara tabbatar da cewa su dangi daya ne wanda babu abin da zai raba kansu.”

Jawabin Sakataren yada labaran na jiya ya kara da cewa: “Ba za mu bari wani abu ya taba hadin kanmu da manufarmu, musamman a irin wannan lokaci a tarihin kasarmu ba.”

"PDP ta fahimci cewa sabanin ya samo asali ne daga tsabar kishin jihohi da kauna da wadannan gwamnoni da mu ke ganin darajarsu, su ke da shi." Inji Uwar jam’iyyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel