Kurunkus: Buhari ya yi karin haske a kan batun tazarcensa

Kurunkus: Buhari ya yi karin haske a kan batun tazarcensa

Fadar Shugaban kasar Najeriya, ta sake jaddada cewa babu wata niyya ko aniya ta shugaban kasar a kan zarcewa mulkin kasar nan a karo na uku. Kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar, Malam Garba Shehu ya sake jaddada matsayar shugaban kasar.

Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, a yi watsi tare da fatali da duk maganganun wadanda ya kwatanta a kafar sada zumuntar zamani da na "masu neman jan hakali".

"Su sake maimaitawa, duk bayanan da ke nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai nemi zarcewa a karo na uku, karya ne," cewar Malam Garba.

Mutum na farko da ya fara bayyana wannan lamarin shi ne fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin bil Adama, Femi Falana. Ya zargi cewa, shugaban kasan na neman zarcewa a karo na uku ne ta hanyar sauya kundin tsarin mulki. Hakan zai bashi damar zarcewar.

DUBA WANNAN: Lamborghini da $5m: An cafke dan shugaban wata cibiyar tarayya a Dubai

Kurunkus: Buhari ya yi karin haske a kan batun tazarcensa

Garba Shehu
Source: Twitter

Sanarwar ta bayyana cewa, Falana na mora ne daga 'yancin fadin albarkacin bakinsa da gwamnatin shugaba Buhari ta tabbatarwa da 'yan kasar Najeriya. Amma baya ga hakan, babu wani dalili na masu matsin da zai sa shugaba Buhari ya amince da batun.

"Babu wani dalili da har zai sa shugaba Buhari ya sauya kundin tsarin mulki don neman karin wani wa'adi. Shugaba Buhari zai kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu ne a 2023, sannan a sake zabe ba tare da ya kara fitowa takara ba."

Sanarwar ta kara da bayyana cewa shugaba Buhari dan dimokaradiyya ne, yana kuma matukar mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya, a don haka kuwa ba zai sabawa tanadin kundin tsarin mulki ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel