Ma’aikata: Gwamnan Oyo ya ce zai saki albashi wata na 13 a Disamba

Ma’aikata: Gwamnan Oyo ya ce zai saki albashi wata na 13 a Disamba

Tun da aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Oyo a Ranar 29 ga Watan Mayu, Seyi Makinde, bai rabu da hawa motar da aka san shi da ita tun kafin ya zama gwamna ba.

Sabon gwamnan bai saye wata sabuwar mota ga jami’an gwamnatin jihar Oyo ba saboda ganin jihar ta cigaba. Gwamnan ya na ganin wannan shi ne irin gudumuwar da za su bada.

Yanzu haka gwamnan ya fito ya yi alkawarin zai biya Ma’aikatan gwamnatin jihar albashi wata na 13. Abin da wannan ya ke nufi shi ne Ma’aikata za su tashi da albashi biyu a Disamba.

Yayin da ake shirin bikin Kirismeti da na shiga sabuwar shekara a halin yanzu, mun fahimci wannan labari da aka ji, ya sa dinbin Ma’aikatan jihar sun fara murna da zuwa albasun.

KU KARANTA: Abin da ya sa PDP ta ki motsawa game da batun takarar Shugaban kasan 2023

Kamar yadda gwamnan ya bayyana a wata hira da ya yi, a dalilin rashin sayen motocin da ya yi, ya adanawa gwamnatin Oyo Naira biliyan 3 zuwa biliyan 4 da aka saba batarwa a baya.

A wani jawabi da gwamnan ya yi ta bakin Mai magana da yawunsa Taiwo Adisa, wanda ya shigo hannunmu, Seyi Makinde ya yi alkawarin cigaba da kula da walwalar mutanen jiharsa.

Game da abin da ya gada daga gwamnatin APC, gwamnan ya bayyana cewa: “A Ranar 6 ga Watan Mayu, gwamnatin baya ta karbi Naira bliyan 5.2, amma aka bar N19, 000 a Ranar 29 ga Wata.”

Mai girma Gwamnan ya kara da cewa: “Ya zama dole ga wadanda su ka yi wannan aiki su fito su yi wa mutane bayani.” Makinde ya ce wannan ya sa ya ci bashin Naira biliyan 10 kwanaki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel