Shugaba Buhari ya dauke wani sabon kwamishina daga gwamnatin Matawalle

Shugaba Buhari ya dauke wani sabon kwamishina daga gwamnatin Matawalle

Sabon kwamishinan kimiyya da fasaha na jahar Zamfara, Alhaji Bilyaminu Shinkafi ya yi murasu daga mukaminsa wanda gwamnan jahar, Bello Matawalle ya nada shi, sa’annan ya amshi tayin mukamin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa.

A tattaunawarsa da jaridar Premium Times, Shinkafi ya bayyana babban dalilin da yasa ya yi fatali da mukamin kwamishinan, inda yace shugaban kasa Buhari ne ya yi masa tayin kwamishinan kasa a hukumar kula da majalisun dokokin Najeriya, inda zai wakilci Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Katsina.

KU KARANTA: Mummunan hatsari ya halaka mutane 19 a jahar Katsina, da dama sun jikkata

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Bilyaminu Shinkafi yana cewa wannan wata dama ce ya samu domin bauta ma jama’ansa yadda ya kamata fiye da mukaminsa na kwamishinan jaha, shi yasa ma ya bai yi wata wata ba ya yi murabus.

Sai dai Bilyaminu Shinkafi ya musanta rade radin da ake yayatawa a jahar Zamfara cewa ya yi fatali da maigidansa Gwamna Bello Matawalle, kuma ya rungumi tafiyar tsohon gwamna Abdulaziz Yari, wanda ake ganin shi ne dalilin samunsa mukamin.

“Na amshi tayin wannan mukami ne saboda kishin kasa, ba tare da la’akari da siyasa ba, yanzu lokaci ne na aiki, kuma dama can ai a kullum ina tare da masu shirin kawo cigaba ne.” Inji shi.

Idan za’a tuna a makon da ta gabata ne shugban yakin neman zaben Gwamna Matawalle, Jamilu Zanna ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishinan ilimi a jahar Zamfara, inda yace ya yi haka ne saboda gwamnan ya gaza wajen cika alkawurran daya daukan ma al’ummar jahar.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mika mulkin jahar Kaduna ga Kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali, a matakin rikon kwarya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel