Seriake Dickson ne silar shan kashin PDP a Bayelsa – Inji Gwamna Wike

Seriake Dickson ne silar shan kashin PDP a Bayelsa – Inji Gwamna Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Takwaransa gwamna Serieke Dickson na jihar Bayelsa, shi ne sanadiyyar tika PDP da kasa da jam’iyyar APC ta yi a zaben kwanaki.

Nyesom Wike ya hakikance a kan cewa babu wanda ya jawowa PDP rashin nasara sai gwamnan na ta. Wike ya yi wannan magana ne lokacin da ya zanta da ‘Yan jarida a Garin Fatakwal jiya.

A cewar Nyesom Wike, abin da gwamnan na Bayelsa ya rika yi daf da zaben, shi ne ya jawo PDP ta dauki kashinta a hannun APC. Wike ya ce Dickson ya hana wasu ‘Yan PDP shiga takarar.

A jawabin na sa na Ranar 23 ga Watan Disamban 2019, Wike ya kuma zargi Abokin aikinsa da tsaida mutumin Yankinsa a matsayin ‘Dan takarar mataimakin gwamna a zaben na 2019.

KU KARANTA: Gwamnan Edo ya tonawa Shugaban APC Oshiomhole asiri

Bugu da kari, Seriake Dickson bai yi dawainiyar kula da gwamnonin PDP da su ka ziyarci jihar domin taya sa yakin neman zabe ba. Wike ya ce shi ya yi hidimar gwamnonin daga aljihunsa.

“Na kalubalanci Dickson, Ni na bada motocin da ya kai gwamnonin PDP Bayelsa a lokacin zabe. Ka hana Sanatoci biyu tsayawa takara. Ka dauko mataimakin gwamna daga shiyyarka.”

“Me ka ke so mutane su yi? Ka na tunanin za su ji dadin abin da ka yi? “Kai ka jawo jam’iyya ta kai kasa. Gwamnan ya kuma tabo maganar rikicin rijiyoyin mai da ake yi tsakanin jihohin biyu.

“A matsayinka na gwamna, akwai abin da bai kamata ka yi ba. Zan kare martabar jihar Ribas. Abin takaici ne. Na fahimci fushinsa, amma bai kamata ya huce takaicinsa a kanmu ba.” Inji sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel