Abun da yasa muke yi wa jama'a rijista - Gwamnatin jihar Kaduna

Abun da yasa muke yi wa jama'a rijista - Gwamnatin jihar Kaduna

Babban sakataraiyar hukumar yi wa mazauna jihar Kaduna rijista (KADSRRA), Elizabeth Joshua, ta ce gwamnatin jihar ta fara rijistar jama'ar dake zaune a jihar ne saboda dalilan tsaro.

Ana sa ran tsarin rijistar mazauna jihar da aka kaddamar a watan Yuni na shekarar 2018 zai taimaka wajen habakar tattalin arzikin jihar da kuma taimaka wa gwamnati wajen samun bayanai a kan jama'arta.

Shugabar hukumar KADSRRA ta bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan jama'a a kan bukatar su rungumi tsarin rijistar domin bawa gwamnatin jihar hadin kai a kokarinta na tsara rayuwar jama'a da kuma kawo cigaba, ta bukaci jama'a su yi dafifi wajen fita domin a yi musu rijista.

Ta ce hukumar KADSRRA tana yin rijistar jama'ar ne bisa hadin gwuiwa da hukumar bayar da katin dan kasa domin bawa gwamnati damar sanin yadda zata raba arzikin da take da shi a tsakanin mazauna jihar.

"Duk wanda zai zauna a jihar Kaduna na tsawon kwanaki 180, watau wata shidda, dole ya mallaki katin rijista, wanda da shi za ake yin amfani wajen biyan ma'aikatan gwamnati albashi da kuma bawa mazauna jihar damar more kayan jin dadin rayuwa da gwamnatin jihar ta samar," a cewarta.

Ta yi kira ga mazauna jihar da su gaggauta mallakar takardar shaidar rijista domin a nan gaba sai mutum ya gabatar da shaidar kafin a karbi dansa ko diyarsa a makarantun gwamnati da kuma masu zaman kansu dake jihar.

Ta bukaci mazauna jihar su ziyarci cibiyoyin yin rijistar da takardunsu na haihuwa, karamin hoto, shaidar rijistar katin dan kasa daga hukumar NIMC da kuma takardar tantance wa kowacce iri domin mallakar katin rijistar hukumar KADSRR.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel