Mun bayyanawa Buhari abinda muka tattauna da Ganduje da Sarkin Kano - Fayemi

Mun bayyanawa Buhari abinda muka tattauna da Ganduje da Sarkin Kano - Fayemi

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa kwamitinsa ta gana da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kan sulhu tsakaninsu.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai ranar Litinin bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari, Fayemi ya ce bangarorin biyu sun nuna niyyar tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Yace: "Kwamitin ta fara aikinta. Za ku tuna cewa na dade ina kokarin ganin a dinke barakar nan a jihar Kano."

"A matsayina na shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya tare da wasu masu ruwa da tsaki a jihar Kano, mun kafa kwamitin sulhu amma yanzu mun fadada kwamitin kuma tsohon shugaban kasa, Janar Abdus Salam Abubakar, ke jagorantanmu."

"Mun kaddamar da tattaunawa da bangarorin biyu kuma mun tabbatar da cewa suna son zaman lafiya tsakaninsu. Mun sanar da Buhari abinda muke nufin yi."

"Duk da cewa ba kwamitin gwamnatin tarayya bane, shugaban kasa ba zai kawar da kai kan wani abin da zai hana zaman lafiya a daya daga cikin jihohi mafi muhimmanci a siyasar kasa ba."

"Dalilin da yasa muka sa baki cikin lamarin shine gwamna Ganduje abokin aikinmu ne a kungiyar gwamnoni. A yanzu haka, zamu sa baki cikin lamarin da faruwa tsakanin abokanmu na jihar Ribas da Bayelsa."

Rikici ya ki ci, ya ki cinyewa tsakanin mai martaba sarkin Kano da gwamnan jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel