Yanzu-yanzu: Gwamnoni sun bukaci a kara duba yanayin kasafin kudin shiga

Yanzu-yanzu: Gwamnoni sun bukaci a kara duba yanayin kasafin kudin shiga

Gwamnonin jihohi 36 na kasar nan sun bayyana bukatarsu ta kara duban tsarin kasafin kudin shiga. Shugaban gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya bayyana hakan a yayin tattaunawa da manema labaran gidan gwamnati bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnan, a yayin da aka bukacesa da ya bayyana matsayar sauran gwamnonin a kan tsarin rabon kudin shigar, wanda shine daya daga cikin sharadinsu kafin su aminta da karin karancin albashi, ya ce: "Kara duba da yanayin tsarin kason kudin shiga har yanzu shine matsayar kungiyar gwamnonin kasar nan."

"Muna tunanin lokaci ya yi da za a duba yanayin tsarin kason kudin shiga, kuma mun mika masu wakiltarmu a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Wannan tsarin ya saba faruwa tun a karkashin mulkin Obasanjo, Shugaba Yar'adua da kuma Shugaba Jonathan. Kawai wannan abu ne da aka kawo karkashin Shugaban kasa Buhari.

DUBA WANNAN: Daya bayan daya: Buhari ya ja 'labule' da gwamnonin APC 3 a fadarsa

"Kuma kamar yadda kuka sani , akwai hnayoyin da ake bi. Hukumar kula da kudin shiga ta RMAFC zata yi iya kokarinta, zata tattauna da masu ruwa da tsaki na kasar tare da wakilanmu. Kowacce jiha tana da wakili a RMAFC kuma a makon da ya gabata ne suka yi taro tare da tattaunawa."

Fayemi ya kara da cewa, "Cewa hakan zai shafi sabon karancin albashin, ba haka bane. Wannan ya riga ya zama doka. Amma kamar yadda na ce, gwamnoni duk sun amince da N30,000 a matsayin sabon albashin, kuma babu wanda zai biya kasa da hakan. Wasu daga cikin gwamnonin na bukatar a kammala wannan tsarin kafin su fara biyan sabon albashin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel