OHCSF ta canzawa manyan Darektoci wurin aiki a Gwamnatin Tarayya

OHCSF ta canzawa manyan Darektoci wurin aiki a Gwamnatin Tarayya

Mun samu labari cewa an canzawa wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin tarayya wurin aiki a Najeriya.

Wannan sauyi da aka yi ya shafi Darektocin gwamnatin tarayya da ke kan mataki na 15 zuwa 17 a wurin aiki.

Gwamnatin tarayyar kasar ta bada wannan sanarwa ne a wata sanarwa da aka fitar a karshen makon jiya.

An fahimci cewa gwamnati ta ba wadanda canjin ya shafa lokaci su yi abin da ya dace ko ayi masu ukuba.

Shugaban ma’aikatar gwamnatin tarayya, Folasade Yemi-Esan ta sa hannu a kan wannan takarda.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi wasu nade-nade a Ma'aikatar sadarwa

OHCSF ta canzawa manyan Darektoci wurin aiki a Gwamnatin Tarayya

Yemi-Esan ta zama HCSF bayan Buhari ya sallami Winifred Oyo-Ita
Source: UGC

Mukaddashiyar shugabar ma’aikatar ta bukaci Darektocin da aka sauyawa wurin aiki su yi maza su bada wuri.

Darektoci 36 da ke kan mataki 17 da Mataimakan Darektoci 45 da ke mataki na 16 aka yi wa canjin.

Sauran wadanda za su bar wuraren aikinsu sun hada da Mataimakan Darektoci 26 da ke kan mataki na 15.

Dr. Yemi-Esan ta ba wadanda wannan canji ya shafa daga nan zuwa 30 ga Watan Disamba su bar ofis dinsu.

Tun Watan Satumba Dr. Folasade Yemi-Esan ta zama shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya ta rikon kwarya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel