Ma'aikatan gidan rediyo da Talabijin Atiku sun koka kan rashin biyansu albashi

Ma'aikatan gidan rediyo da Talabijin Atiku sun koka kan rashin biyansu albashi

Ma'aikatan gidan Rediyo da Talabijin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, GOTEL, sun koka kan rashin biyansu albashi tun watan Satumban 2019. Premium Times ta ruwaito.

Gotel ce kamfanin Atiku mafi girma cikin kamfanonin da ya mallaka.

Sabanin kamfanin sadarwan Gotel, Atiku ne mammalakin kamfanin ruwan gora da lemu Adama Beverages, jami'ar Amurka ABTI da kuma masana'antar sarrafa shinkafa, Rico Gado.

Kafin watan Satumba, ma'aikatan suk koka kan rashin biyansu albashin watannin Yuli, Agusta da Satumba.

Ma'aikatan kamfanin sun bayyanawa Premium Times cewa, bayan sallamar kimanin rabin ma'aikatan kamfanin a shekarar 2016 da Najeriya ta shiga matsin tattalin arziki, ba'a taba karawa sauran ma'aikatan albashi.

DUBA NAN: Ana artabu tsakanin Soji da yan ta'adda a Biu

Sukace: "Ma'aikata basu san halin da suke ciki ba. Shin zasu dogara a yarjejeniyar da akayi a baya na ko wanne? Ma'aikatan da ba'a sallama ba a baya basu samu hakkokinsu ba har yanzu."

"Bamu san lokacin da za'a biya albashi ba. Ma'aikatan Gotel na bin bashin albashin watan Oktoba, Nuwamba, da Disamba."

Yayinda aka tuntubi, Paul Ibe, mai magana da yawun Atiku Abubakar, ya ce ba zai iya tsokaci kamn lamarin ba saboda ya daina aiki a Gotel.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel