Sai APC ta fitar da matsaya game da 2023 sannan PDP za ta dauki mataki

Sai APC ta fitar da matsaya game da 2023 sannan PDP za ta dauki mataki

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta na yunkurin shawo karshen rikicin cikin-gidan da ya ratsa jam’iyyar tare da karfafa jam’iyyar kafin zabe mai zuwa.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa jam’iyyar hamayyar za ta gyara cikin gidanta kafin ta tsaida matsaya game da yankin da zai fito da shugaban kasa a 2023.

A zaben bana, PDP ta fito da ‘Dan takararta na shugaban kasa ne daga Arewacin Najeriya. A karshe ‘Dan takarar da aka tsaida ya sha kashi a hannun APC.

Wannan rashin nasara da Atiku Abubakar ya samu a zaben 2019 ya sa aka tado maganar Yankin da zai rikewa jam’iyyar ta PDP tuta a zaben da za ayi a 2023.

Jaridar ta ce ta samu labarin cewa Jagororin PDP su na bi sannu a hankali ne kan batun takarar shugaban kasar saboda gudun ‘Ya ‘yan jam’iyyar su canza sheka.

KU KARANTA: Buhari ya fadi abin da ya sa manyan kasa ke fada da shi

Wani daga cikin jiga-jigan jam’iyyar a Arewa maso Gabashin Najeriya, ya shaidawa Majiyar cewa PDP na jiran gudun ruwan APC ne kafin ta yanke hukunci.

Shugaba Prince Uche Secondus da majalisarsa ba za su dauki mataki game da yadda za a tsara takarar 2023 sai jam’iyyar APC mai mulki ta nuna irin lagonta.

PDP za kuma ta tuntubi tsofaffin shugabannin kasar kafin daukar mataki a kan batun takarar. A cewar jam’iyyar ba ta fara zama a kan zaben 2023 ba tukuna.

Legit.ng ta na kyautata zaton daga cikin wadanda za su nemi takarar shugaban kasa a PDP a 2023 akwai Rabiu Kwankwaso, Bukola Saraki da Aminu Tambuwal.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel