Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabbin nade-nade a wasu hukumomi da ke karkashin ma’aikatar sadarwa ta kasa.

Mai ba Shugaban kasa shawara na musamman a kafar sadarwa ta zamani da kafofin watsa labarai, Femi Adesina a wani jawabi ya bayyana cewa hakan na daga cikin manufar Shugaban kasa na saurin cika kudirin ma’ikatar.

Wadanda aka nada sune:

Farfesa Adeolu Akande zai maye gurbin Sanata Olabiyi Durojaiye a matsayin shugaban kwamishinonin hukumar NCC.

Mista Uche Onwude zai maye gurbin Sanata Ifeanyi Godwin Ararume a matsayin Kwamishina daga yankin Kudu Maso Gabas.

Hukumar NITDA – Dr Abubakar Sa’id da ya maye gurbin Farfesa Adeolu Akande a matsayin shugaba. Dr Habibu Ahmed Imam (arewa maso yamma) inda ya maye gurbin Dr Lawal Bello Moriki da Dr Mohammed Sa’idu Kumo a matsayin mamba na hukumar.

Hukumar aika wa wasiku da sakonni (NIPOST) – An nada Dr Ismail Adebayo Adewusi, shugaban Hukumar ina yam aye gurbin Barrister Bisi Adegbuyi .

Hukumar Galaxy Backbone Limited (GBB) - An nada farfesa Muhammed Bello Abubakar ina yam aye gurbin Architect Yusuf Kazaure.

Hukumar The Nigeria Communications Satellite Limited (NigComSat) - An nada Architect Yusuf Kazaure a matsayin shugaban kwamitin hukumar zai maye gurbin Cif Dr George Nnadubem Moghalu.

Dr Najeem Salam zai maye gurbin Hon. Samson Osagie a matsayin darektan kasuwanci da ci gaban hukumar.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Jami’ar Abuja ta fatattaki dalibai 100

Farfesa Abdu Ja’afaru Bambale zai maye gurbin Kazeem Kolawole Raji a matsayin Babban darekta. Hadi Mohammed zai canji Mohammed Lema Abubakar a hukumar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel