Dan majalisar da muka garkame ya kai mamaya ofishin yan sanda da yan daba 50 – Yan sanda

Dan majalisar da muka garkame ya kai mamaya ofishin yan sanda da yan daba 50 – Yan sanda

Rundunar yan sandan jihar Lagas ta ce ta kama Shina Peller, wani dan Majalisar wakiltan kuma mamallakin gidan rawan Quilox kan kai mamaya wani ofishin yan sanda ba bisa ka’ida ba.

Rundunar yan sandan ta ce Mista Peller ya hada yan daba 50 domin kai mamaya ofishin yan sandan Makoro da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, domin daukar motoci uku da aka kwace a gidan rawansa bisa laifin hada cunkoso ta karfin tuwo.

Bala Elkana, kakakin yan sandan Lagas, ya ce an kama Mista Peller tare da yan daba biyar kan laifin kai mamaya.

A cewar jawabin, jami’an yan sanda dake kan kula da cunkoson ababen hawa a hanyar Ozumba mbadi, Victoria Island, sun tura Wani rahoton cunkoso zuwa ya ofishin yan sandan Moroko a ranar Lahadi, cewa hanyar da ke sada mutum da toll gate gaba daya ya toshe sakamakon pakin motoci da kwastamomin Quilox suka yi ba bisa ka’ida ba a hanyar.

Bisa ga rahoton, Shugaban yan sandan reshen Maroko ya sanar da Mista Peller “kan bukatar tabbatar da ganin cewa kwastamomin gidan rawansa ba su toshe babban hanyar ba domin gudun Jefa sauran masu amfani da hanyar cikin mawuyacin hali,” inji yan sandan.

“Sai yan sanda suka warware cunkoson sannan dan Majalisar ya yi alkawarin cewa ba za a cunkushe hanyar ba."

Mista Elkana ya ce da misalin karfe 8:30 na safiyar Litinin, sai aka Kira cewa hanyar ya sake cushewa sannan yan sanda suka sake gano cewa gidan rawan ne ya sake haddasa cunkoson.

“Lamarin ya munana har sai da ya kai masu wucewa sun koma tafiya da kafa,” inji shi.

Domin magance cunkoson, sai aka zuba jami’an reshen Maroko zuwa unguwanni, “sai aka kwashe motoci uku da wasu kwastamomin gidan rawan suka ajiye akan babban titin, wanda hakan sune suka haddasa cunkoson zuwa ofishin yan sandan.”

Mista Elkana ya bayyana cewa jami’an yan sandan da ke aiki a reshen sun aika sako mai cike da damuwa zuwa ga rundunar reshen jihar, don haka aka tura wasu jami’ai daga ofishin da ke kusa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tsare wani dan majalisar wakilai, Shina Peller

Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Hakeem Odumosu, ya yi umurnin cewa a tura lamarin zuwa ga sashin binciken masu laifi na jihar, Yaba, domin bincike a tsanaki.

"Za a tura masu laifin zuwa kotu," inji yan sandan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel