Daya bayan daya: Buhari ya ja 'labule' da gwamnonin APC 3 a fadarsa

Daya bayan daya: Buhari ya ja 'labule' da gwamnonin APC 3 a fadarsa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da shugaban kungiyar gwamnoni, Dakta Kayode Fayemi, a fadarsa. Kazalika, shugaba Buhari ya gana da shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Buhari ya gana da gwamnonin ne daya bayan daya a fadarsa, Villa, dake Abuja.

Buhari ya fara gana wa ne, a bayan fage, tare Fayemi, gwamnan jihar Ekiti.

Daga bisani Buhari ya gana da gwamna Bagudu wanda ya samu rakiyar takwaransa, gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar.

NAN ta rawaito cewa manema labarai basu samu wani rahoto a kan dalilin ganawar Buhari da gwamnonin ba.

DUBA WANNAN: Bayan shan mugun kaye a kotun koli, wani dan takarar gwamna ya koma APC

Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta ce babu wani aibu idan akwai 'miyagu' zagaye da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Fadar ta bayyana cewa, akwai irin mutanen a kowacce gwamnati a fadin duniya.

Fadar ta kara da jaddada cewa, akwai bukatar a kafa dokar soshiyal midiya, ganin cewa rashinta na kawo cin zarafi ga mutane.

Babban mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa a kan yada labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce, "Babu gwamnatin da aka taba samu a kasar nan da babu wasu mutane da ake zargi da zama miyagu a gwamnatin. Kuma hakan ya zama dole ne saboda kowacce gwamnati ko shugaban kasa yana da mataimaka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel