Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tsare wani dan majalisar wakilai, Shina Peller

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun tsare wani dan majalisar wakilai, Shina Peller

- Rahotanni sun kawo cewa rundunar yan sanda a jihar Lagas ta kama da kuma tsare wani dan Majalisar wakilai, Shina Peller

- Anyi zargin cewa an kama Peller, wanda ke wakiltan mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajo, jihar Oyo, yayinda yake kokarin belin wasu da aka kama a gidan rawa

- Dan Majalisar ya kasance mamallakin wani shahararren gidan rawa da ke Lagas, Quilox

- Zuwa yanzu jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Jihar, Bala Elkana, bai amsa kiran wayarsa ba tukuna sannan bai amsa sakon waya da aka tura masa ba kan lamarin

Rahotanni sun kawo cewa rundunar yan sanda a jihar Lagas ta kama da kuma tsare wani dan Majalisar wakilai, Shina Peller, a ofishin yan sandan Moroko.

Anyi zargin cewa an kama Peller, wanda ke wakiltan mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajo, jihar Oyo, yayinda yake kokarin belin wasu da aka kama a gidan rawa.

Dan Majalisar ya kasance mamallakin wani shahararren gidan rawa da ke Lagas, Quilox.

A wani jawabi daga sakataren labaran Peller, ya yi ikirarin cewa ba a bayyana wa dan majalisar laifinsa ba yayinda aka kwace wayoyinsa.

Ya ce: “Peller ya kasance a ofishin yan sandan domin belin wasu kwastamomin gidan rawa na Quilox wanda ake zargin sun ajiye motocinsu a hanya a lokacin wani shiri a gidan rawan.

“Kafin fara shirin wanda ke shafe sa’o’i 36 ba tare da tsayawa ba wanda akan yi duk shekara a Quilox, Peller ya sanar da hukumomin da ke kula da cunkoson ababen hawa na Lagas domin guje ma cunkoso mara tushe.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace wani dan kwamishinan Bayelsa mai shekara 6

“A lokacin da ya isa tashar yan sandan Moroka, sai yan sandan suka fara cin zarafin Peller harma ya kai sun kwace dukkanin wayoyinsa ba tare da dalili ba.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Jihar, Bala Elkana, bai amsa kiran wayarsa ba tukuna sannan bai amsa sakon waya da aka tura masa ba kan lamarin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel