Mummunan hatsari ya halaka mutane 19 a jahar Katsina, da dama sun jikkata

Mummunan hatsari ya halaka mutane 19 a jahar Katsina, da dama sun jikkata

Akalla mutane 19 ne suka gamu da ajalinsu a sakamakon wani mummunan hadari daya auku a kan babbar hanyar Funtua zuwa Zaria, a jahar Katsina, inda mutane da dama suka samu munanan rauni.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito hatsarin ya auku ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba da misalin karfe 8 na dare a daidai marabar Maska inda motoci guda uku suka yi arangama, motocin sun hada da Tankar mai, Sharon da Bus.

KU KARANTA: Sulhu alheri ne: Kalli manyan mutane 10 da zasu shiga tsakanin Ganduje da Sarki Sunusi

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa babbar motar dakon man fetir ce ta kufce ma direbanta, da haka ta afka ma motar Sharon dake makare da fasinjoji, ana cikin haka sai motar Bus ta afka cikin musu gaba daya.

“Mun kirga gawarwaki goma sha tara wanda Yansanda suka kwashesu tare da hadin gwiwar jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC, sai da suka yi sawu 9 daga nan zuwa asibitin Funtua, akwai kuma mutane 7 da suka samu munana rauni da yanzu haka a ka garzaya dasu babban asibitin Funtua.” Inji shi.

Da majiyarmu ta tuntubi shugaban FRSC reshen jahar Katsina, Ali Tanimu sai yace yana kan hanyar zuwa inda hatsarin ya auku, kuma zai bayar da jawabi da zarar ya isa wajen, sai dai har lokacin tattara wannan rahoto babu amonsa.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da wata sabuwar farmaki a kauyen Kaure dake cikin mazabar Kwaki na karamar hukumar Shiroro a jahar Neja, inda suka kashe mutane 8 nan take.

Kansilan mazabar Kwaki, Malam Jafaru Kwaki ya tabbatar da harin, inda yace da misalin karfe 8 na safiyar Lahadi, 22 ga watan Disamba ne yan bindigan suka shiga kauyen a kan babura suna ta harbe harbe.

“Na samu labarin sabon harin da yan bindiga suka kaddamar a garinmu, rahotanni sun tabbatar min da cewa yan bindigan suna sanye da bakaken kaya ne. sun shiga kauyen ne a kan babura suna harbin mai kan uwa da wabi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel