Bayan shan mugun kaye a kotun koli, wani dan takarar gwamna ya koma APC

Bayan shan mugun kaye a kotun koli, wani dan takarar gwamna ya koma APC

- Bayan shan kayen Abiodun Akinlade a kotun koli, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

- Akinlade ya sanar da wannan hukuncin da ya yanke ne na komawa APC daga APM a yau Litinin

- Akinlade ya fito takarar shugabancin jihar Ogun ne a karkashin jam’iyyar APM a 2019

Kwanaki kadan baya shan mugun kaye da dan takarar gwamnan jihar Ogun karkashin jam’iyyar APM, Abiodun Akinlade ya yi, ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC a yau Litinin, 23 ga watan Disamba, 2019.

Ana zafin yakin neman zabe ne Akinlade ya canza sheka zuwa APM inda ya yi takarar kujerar gwamnan jihar tare da Dapo Abiodun, wanda shi ne dan takarar da yayi nasarar lashe zaben fidda gwani a jam’iyyar APC.

DUBA WANNAN: Ba laifi bane don 'miyagu' sun kewaye Buhari - Fadar shugaban kasa

Abiodun ne yayi nasarar lashe zaben inda Akinlade ya garzaya kotun sauraron kararrakin zabe. A nan ya fara shan kaye. Akinlade ya daukaka kara inda a can ya sha kasa, kafin daga bisani ya garzaya kotun koli. Hakazalika, hukuncin bai sauya ba, don Abiodun ya kara nasara inda aka yi watsi da koken Akinlade.

Kotun kolin ta yanke hukuncin cewa, Akinlade ba shi da gamsasshiyar hujja a kan zargin da yake ga Gwamna Abiodun na jam’iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel