Ba laifi bane don 'miyagu' sun kewaye Buhari - Fadar shugaban kasa

Ba laifi bane don 'miyagu' sun kewaye Buhari - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta ce babu wani aibu idan akwai 'miyagu' zagaye da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Fadar ta bayyana cewa, akwai irin mutanen a kowacce gwamnati a fadin duniya.

Fadar ta kara da jaddada cewa, akwai bukatar a kafa dokar soshiyal midiya, ganin cewa rashinta na kawo cin zarafi ga mutane.

Babban mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa a kan yada labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce, "Babu gwamnatin da aka taba samu a kasar nan da babu wasu mutane da ake zargi da zama miyagu a gwamnatin. Kuma hakan ya zama dole ne saboda kowacce gwamnati ko shugaban kasa yana da mataimaka.

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun kai hari a kan ma'aikatan 'jin kai', sun kashe 3 tare da raunata 2

"Kowanne shugaban kasa yana da masu bashi shawara. Ba laifi bane, kuma ba zai zama zunubi ba don kana da mutanen da ka yadda dasu. A kowacce kasa akwai su, a nan ne ake kiransu da miyagu don bata su da aiyukan alherinsu." Cewar Shehu.

Shehu yace da yawa daga cikin mutanen da ake kira da miyagu a wannan gwamnatin, mutane ne da suka samu matukar nasara. Suna kokari wajen bautawa gwamnatin nan.

Ya ce: "Wasu daga cikinsu basu da bukatar zama tare da gwamnatin. A takaice, ga masu hannu da shuni a kasar nan, Shugaban kasa bashi da kirki saboda ba zaka iya zuwa gabanshi ka ce ya baka rijiyar man fetur ba. Ba zai sa maka hannu kan takarda kai tsaye ba."

A yayin bayani a kan daidaita kafafen sada zumuntar zamani, Shehu ya jajanta cewa soshiyal midiya ta zama babbar matsala ga iyalai saboda hakkokin mata da kananan yara da ake takewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel