Yan bindiga sun sace wani dan kwamishinan Bayelsa mai shekara 6

Yan bindiga sun sace wani dan kwamishinan Bayelsa mai shekara 6

- Yan biniga sun kai farmaki kwatas din sabbin kwamishinoni a Yenagoa a ranar Lahadi, 23 ga watan Disamba sannan suka sace yaron wani kwamishina mai shekara shida

- An tattaro cewa maharan sun sace yaron ne bayan kwamishinan ya ce lallai shi baida kudin basu

- Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Asinim Butswat, ya tabbatar da lamarin, ya kuma bayyana cewa sun baza jami'ansu domin ceto yaron tare da kama masu laifin

Wasu yan bindiga hudu da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki kwatas din sabbin kwamishinoni a Yenagoa a ranar Lahadi, 23 ga watan Disamba sannan suka sace yaron wani kwamishina mai shekara shida.

An bayyana yaron a abun ya cika dashi a matsayin dan kwamishinan ruwa, Nengi Talbot.

An tattaro cewa yan bindigan sun fasa kai gidan Talbot da ke kwatas a Opolo sannan suka bukaci kwamishinan ya basu kudi.

Wata majiya, wacce ta yi magana bisa sharadin sakaya sunanta, ta ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 11 na dare inda ta kara da cewa maharan sun sace yaron lokacin da kwamishinan ya ce lallai shi baida kudi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Asinim Butswat, ya tabbatar da lamarin.

Ya ce: “A ranar 22 ga watan Disamba da misalin 11:30 na dare, kimanin yan bindiga hudu sun kai mamaya gidan kwamishinan ruwa, Hon. Nengi Talbot, a kwatas din sabbin kwamishinoni da ke Opolo, Yenagoa, sannan suka sace dansa mai shekara shida zuwa wani wuri da ba a sani ba.

KU KARANTA KUMA: Saudiyya ta yanke wa mutane 5 hukuncin kisa kan kisan Jamal Khashoggi

“Rundunar ta kaddamar da farauta domin ceto yaron da kuma kama masu laifin. Ana kan bincike.”

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnatin tarayya ta ce akwai alamu da ke nuna cewa yan ta’addan Boko Haram na iya kai hari da makamai masu guba wadanda ake kira da chemical, biological, radiological, nuclear and explosive (CBRNE) a nan gaba.

A cewar jaridar Punch, hakan na kunshe ne a cikin takada mai shafi 60 mai taken “National Security Strategy” wato “Dabaran tsaron kasa”, wanda ofishin mai ba kasa shawara a harkar tsaro ta saki a baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel