Yanzu-yanzu: Ka cigaba da zama a gidan yari - Kotu tayi watsi da bukatar belin Orji Kalu

Yanzu-yanzu: Ka cigaba da zama a gidan yari - Kotu tayi watsi da bukatar belin Orji Kalu

Alkali mai shari'a, Jastis Mohammed Liman, na babban kotun tarayya ya yi watsi da bukatar belin Sanata Orji Uzor Kalu kan rashin lafiya.

A cewar Alkalin, Orji Uzir Kalu bai gabatar da isassun hujjojin da zai sa kotun ta bashi beli ba bayan an garkameshi a gidan gyara hali.

Alkalin ya kara da cewa babu kwakkwarin hujjan cewa Kalu na fama da ciwo mai tsanani irinsu ciwon siga ko hawan jini, kuma wani bai iya kamuwa da cutar.

Bugu da kari, Jasits Liman ya ce lallai al'ummar Abia ta Arewa da yake wakilta a majalisar dattawa za suyi rashinsa amma su suka debo ruwan dafa kansu saboda sun sani sarai ana gurfanar da shia kotu kafin suka zabesa ya wakilcesu.

A ranar Talata, 17 ga Disamba, 2019 Tsohon gwamnan da babbar kotun tarayya dake Legas ta yankewa hukuncin shekaru 12 a gidan yari ya bukaci kotu ta sake bashi beli.

Kalu ya bayyanawa kotu cewa yana bukatan belin ne saboda yana fama da rashin lafiya kuma ba zai iya samun isasshen kula daga asibitin dake cikin kurkukun ba, saboda haka yana bukatar bokansa.

Hakazalika, ya bayyanawa kotu cewa mazabarsa da yake wakilta a majalisar dattawa za tayi rashi babba idan ya cigaba da kasancewa cikin kurkuku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel