Saudiyya ta yanke wa mutane 5 hukuncin kisa kan kisan Jamal Khashoggi

Saudiyya ta yanke wa mutane 5 hukuncin kisa kan kisan Jamal Khashoggi

- Wata kotun Saudiyya ta yanke wa mutane biyar hukuncin kisa bayan samun su da hannu dumu-dumu a kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi

- An kuma yanke wa wasu uku shekaru 24 a gidan yari kan rawar ganin da suka taka wajen kisan

- Kotun ta kuma yanke cewa ba a samu jakadan Saudiyya a Istanbul a wancan lokacin, Mohammed al-Otaibi, da laifi ba

Ofishin da ke gabatar da kararraki na kasar Saudiyya, ta bayyana cewar an yanke wa mutane biyar hukuncin kisa sannan kuma aka yanke wa wasu uku shekaru 24 a gidan yari kan rawar ganin da suka taka wajen kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a shekarar da ta gabata.

An samu dukkanin da aka gurfanar da hannu dumu-dumu a kisan, wanda hakan ya haddasa babban rikicin diflomasiyya na birnin yayinda shugabannin duniya da manyan yan kasuwa suka nesanta kansu daga Riyahd.

Sai dai kuma, tashar talbijin na Saudiyya ta kuma ruwaito cewa binciken babban atoni janar na Saudiyya ya nuna cewa tsohon babban mai ba yarima Mohammed bin Salman shawara, Saud al-Qahtani, bai da hannu a kisan, bayan an bincike shi sannan aka sake shi ba tare da wani tuhuma ba.

Kotun ta kuma yanke cewa ba a samu jakadan Saudiyya a Istanbul a wancan lokacin, Mohammed al-Otaibi, da laifi ba. Don haka aka sake shi daga gidan yari bayan an sanar da hukuncin.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Jami’ar Abuja ta fatattaki dalibai 100

Kafin kisan nasa, Khashoggi ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin kasar Saudiyya kuma wasu jam'ian gwamnatin Saudiyyar ne suka kashe shi a offishin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul na Turkiyya.

Agnes Callamard a kwanakin baya ta yi kira da a binciki yariman Saudiyya Mohammed bin Salman kan kisan Jamal Khashoggi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel