Tirkashi: Jami’ar Abuja ta fatattaki dalibai 100

Tirkashi: Jami’ar Abuja ta fatattaki dalibai 100

- Jami’ar Abuja ta sanar da fatattakar dalibai 100 kan rashin bin ka’idar jarrabawa

- Daliban da lamarin ya shafa sun hada da masu karatun mallakar takarar digiri 72 da masu karatun digiri na biyu su 28

- Ya kara da cewa an umurci daliban da lamarin ya shafa da su mika duk wani kaya da ya kasance mallakin jami’ar wanda ke a hannunsu ciki harda katin shaidarsu zuwa ga Shugaban sashinsu, sannan kuma su yi gaggawan barin makarantar

Jami’ar Abuja a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba ta sanar da fatattakar dalibai 100 kan rashin bin ka’idar jarrabawa.

Jami’ar tace wadanda aka kora sun hada da masu karatun mallakar takarar digiri 72 da masu karatun digiri na biyu su 28.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin jami’ar, Habib Yakoob, ya bayyana cewa an dakatar da wasu dalibai biyar da ke karatun digiri na tsawon zangon karatu guda.

Ya ce an kuma dakatar da wasu mutum uku da ke karatun digiri na biyu tsawon zangon karatu guda.

A cewarsa, majalisar dattawan jami’ar a zamanta na 174 da ya gudana a ranar 6 ga watan Nuwamba ta aiwatar da rahoto da shawarwarin kwamitin rashin bin ka’idar jarrabawa sannan bayan tattaunawa, ta amince da korar daliban.

Ya kara da cewa an umurci daliban da lamarin ya shafa da su mika duk wani kaya da ya kasance mallakin jami’ar wanda ke a hannunsu ciki harda katin shaidarsu zuwa ga Shugaban sashinsu.

KU KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar Boko Haram ta yi amfani da makamai masu guba a nan gaba - FG

Ya ce an kuma shawarci daliban da su yi gaggawan barin makarantar.

Mista Yakoob ya ce duk dalibin da ya take doka da tsarin makarantar zai fuskanci hukuncin da ya dace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel