Yanzu-yanzu: An karawa manyan jami'an yan sanda 623 girma

Yanzu-yanzu: An karawa manyan jami'an yan sanda 623 girma

Hukumar kula da jami'an yan sandan Najeriya wato Police Service Commission (PSC) ta rattafa hannu kan karawa manyan jami'an yan sanda 623 girma.

Hakazalika an karawa mataimakan kwamishanoni DCP 40 girma zuwa matsayin kwamishana CP.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana hakan ne jiya inda ya zayyana cewa kananan mataimakin kwamishana ACP sun samu matsayin DCP, Cif Sufritandan 150 sun koma ACP, kuma kananan Sufritandan 335 sun zama Cif Sufritandan.

Ani ya bayyana cewa an karawa yan sandan girma ne bisa ga kokari, jarunta da cike gurbi.

A wani labarin daban, Shugaba Buhari ya jaddada cewa za'a rika daukan sabbin jam'in yan sanda 10,000 a kowani shekara domin karfafa tsaro.

Buhari ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da sabbin motocin hukumar sama da 200 a birnin tarayya Abuja.

Jawabin Buhari ya biyo bayan hukucin babban kotun tarayya da ke Abuja inda ta yi fatali da karar da ke kalubalantar shugaban 'yan sandan Najeriya na diban 'yan sanda 10,000 aiki a fadin kasar nan.

A yayin yanke hukunci, Jastis Inyang Ekwo ya ce, hukumar 'yan sandan karkashin jagorancin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya na da karfin ikon fitar da jerin sunayen mutanen da ta dauka aiki a hukumar.

Mai shari'a Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yi watsi da karar da hukumar kula da aiyukan 'yan sanda (PSC), ta miko gabanta na kalubalantar ikon IGP da ya dauka sabbin jami'ai aiki a hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel