CJN: Fita batun shari’a, ka nemi ayi wa Najeriya garambawul – Ahmed Gumi

CJN: Fita batun shari’a, ka nemi ayi wa Najeriya garambawul – Ahmed Gumi

Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abububar Mahmud Gumi, ya yi magana game da kiran da Alkalin Alkalan Najeriya ya yi game da sha’anin shari’a.

A wajen wani taro, Alkalin Alkalan kasar, Muhammad Tanko, ya nemi a rika aiki da dokokin shari’a. Wannan kira ya jawo surutu musamman daga Mabiya sauran addinai.

A na sa ra’ayin Ahmad Abububar Mahmud Gumi ya na ganin cewa yi wa tsarin Najeriya garambawul shi ne babbar mafita ba kawo shari’ar musulunci a Najeriya ba.

“Abin da na ke ganin ya dace mu yi shi ne a sakewa Najeriya zani, ta yadda bangarorin da Muslumai su ka fi yawa irinsu Kano da Zamfara, za su yi abin da su ke so…”

Babban Malamin Musuluncin ya cigaba da cewa: “Wuraren da Kiristoci su ka fi yawa, sai a kyalesu su yi abin da su ke so.” A na sa hangen wannan shi ya fai dacewa.

KU KARANTA: Mutanen da za su sasanta Ganduje da Sarki Sanusi II a Kano

CJN: Fita batun shari’a, ka nemi ayi wa Najeriya garambawul – Ahmed Gumi

Sheikh Ahmad Abububar Mahmud Gumi ba ya goyon bayan CJN
Source: UGC

“Ka da ka yi maganar shari’a. Kowace jiha ta samu gashin kan-ta, wanda zai bata damar yin abin da zai taimaki mutanenta. Ba za ka yi watsi da addini ba, ya na da tasiri.”

“Amma idan aka yi amfani da addini wajen juya hankalin mutane, to ya zama hadari. Idan kuma aka yi amfani da addini yadda Ubangiji ya yi umarni, hakan ya yi kyau.”

Gumi ya cigaba da cewa: “A Musulunci, an ce Musulmi ya kaunaci Kirista. Ka da a kakaba shari’a ga kowa a kasar nan, a bar jihohin Musulmai su yi amfani da shari’ar su.”

Malamin ya bayyana cewa kawo shari’a da aka yi a Zamfara, ya rage laifuffuka a jihar. Gumi ya ce kasar Saudi ta na aiki da shari’a, amma bai hana kasar ta kawo cigaba ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel