Sulhu alheri ne: Kalli manyan mutane 10 da zasu shiga tsakanin Ganduje da Sarki Sunusi

Sulhu alheri ne: Kalli manyan mutane 10 da zasu shiga tsakanin Ganduje da Sarki Sunusi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shirin kawo sasanci tare da sulhunta tsakanin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje tare da mai martaba Sarkin, Muhammadu Sunusi II.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito takun saka tsakanin gwamnan da Sarkin ya zurfafa ne tun bayan da gwamnan ya kirkiri sabbin masarautu guda hudu, kuma ya daga likafarsu zuwa masu daraja ta daya, daidai da na Sarki Sunusi.

KU KARANTA: Manyan Najeriya na fada da Buhari ne ba don komai ba sai don rijiyar mai – Garba Shehu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka wani kwamiti da ya samu cikakken goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara aikin sasanta shuwagabannin biyu, kamar yadda sakataren kwamitin, Adamu Fika ya bayyana.

“Duba da rikicin dake faruwa a Kano, wanda idan aka yi wasa zai iya kaiwa ga matsalar tsaro a jahar, har ma ya tsallaka zuwa jahohin dake makwabtaka da Kano, a yanzu dai an kafa wata kwamitin manyan kasa a karkashin jagorancin Janar Abdulsalam Abubakar domin su sasanta rikicin tare da kawo karshensa.” Inji shi.

Adamu Fika ya bayyana sauran mambobin kwamitin kamar haka:

- Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi

- Gwamna Aminu Bello Masari

- Janar Muhammadu Inuwa Wushishi

- Alhaji Abdullahi Ibrahim SAN

- Dakta Dalhatu Sarki Tafida

- Dakta Umaru Mutallab

- Farfesa Ibrahim Gambari

- Sheikh Sharif Saleh

Sakataren kwamitin, Adamu Fika, wazirin Fika ya cigaba da fadin: “Kwamitinmu na aiki da sanin gwamnatin tarayya, kuma mun fara zama da gwamnan, sa’annan mun zauna da Sarkin, inda muka nemi kowa ya mayar da wukarsa cikin kube.

“Kuma dukkansu sun yi alkawarin jan hankulan masoyansu da magoya bayansu musamman na shafukan sadarwar zamani daga furta wasu kalaman batanci, wakoki ko kuma rubuce rubuce da zasu iya kawo matsala ga aikin sulhun da muke yi.

“Da fatan Allah Ya taimakemu, Ya taimaki kasarmu, Ya bamu zaman lafiya da cigaban arziki, muna addu’ar Allah Ya albarkaci shuwagabanninmu, Ya shiryar dasu, Ya kuma karesu, Amin.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel