Yadda rade-radin ‘auren’ Shugaba Buhari ya zagaye Najeriya kwanaki

Yadda rade-radin ‘auren’ Shugaba Buhari ya zagaye Najeriya kwanaki

A cikin Watan Oktoban 2019 ne labari ya gama ratsa ko ina cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kara aure, inda zai angonce da Ministarsa, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

A tsakiyar makon da aka yada cewa za ayi wannan aure, maganar ta shiga lungu da sakon Najeriya. Babu wanda ya iya tabbatar ko ya korewa rade-radin wannan daurin aure.

The Nation ta kawo rahoto cewa mutane har sun kirkiro irin kayan da jama’a za su sa a ranar wannan babban biki. An kuma zabi masallacin da aka ce a nan za a daure auren.

A al’ada da addini dai Wakilan Ango su kan tafi wurin Dangin Amarya ne su ka karbi aure a hannun Waliyyinta. Da kuwa da gaske za ayi auren, da za a tafi Garin ita Matar ne.

Wannan rade-radi ya sa mutane su ka cika babban masallacin Juma’a da ke Abuja. Har da manyan Ministoci aka gani da tunanin cewa wanan ranar da ake ta magana ta zo.

KU KARANTA: Abin da ya sa manyan kasa ba su kaunata - Shugaba Buhari

Yadda rade-radin ‘auren’ Shugaba Buhari ya zagaye Najeriya kwanaki

Aisha Buhari ta ce Sadiya Faruk ba ta yi tunanin ba za ayi auren ba
Source: Facebook

Abin da ya kara rikitar da jama’a shi ne gum din da fadar shugaban kasa da Ministar su ka yi. A wani shafin bogi ne kurum aka samu wata ta sunan Ministar ta na karyata batun.

A Ranar Juma’a 11 ga Watan Oktoban, wani Minista ya yi wa ‘Yan jarida dariya ganin yadda su ka cika masallacin, yayin da wani ya yi masu ba’ar ba za a bar kowa ya shiga ba.

Bayan an kammala sallar Juma’a a masallacin da ke fadar shugaban kasa da na cikin Garin Abuja, jama’a ba su ji wata sanarwar cewa shugaban kasa Buhari zai yi aure ba.

Daga nan ne mutane su ka fara fahimtar cewa a dandalin sada zumunta kawai aka yi wannan aure aka gama. Dama can duk wanda ya ga katin auren, ya san cewa na bogi ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel