Wasu Kiristocin Arewa sun roki Shugaba Buhari ya kubuto da Leah Sharibu

Wasu Kiristocin Arewa sun roki Shugaba Buhari ya kubuto da Leah Sharibu

Wata kungiya ta Mabiya addinin Kirista a Arewacin Najeriya mai suna NOSCEF ta bukaci Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kubutar da da Miss Leah Sharibu.

Kungiyar NOSCEF ta Dattawan Kiristocin da ke Arewacin kasar nan sun bayyana cewa ceto wannan Yarinya daga hannun ‘Yan ta’adda shi ne zai zama tukuicin kirismetinsu.

The Nation ta kawo rahoto cewa wannan kungiya ta bakin shugabanta, Ejoga Inalegwu, ta fitar da jawabi na musamman game da wannan 'Yar makaranta da Boko Haram su ka tsare.

“Mu na rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba al’ummar Kiristocin wannan babbar kasa Najeriya goron Kirismeti, ta hanyar kubuto da Yarinyarmu Leah Sharibu.”

Shugaban kungiyar ya lallabi shugaban kasar ya yi kokarin ganin wannan 'Dalibar da Boko Haram su ka sace tun 2018, ta dawo gida a bikin Kirismetin wannan shekarar.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun yi kokarin shiga cikin Damaturu

Ejoga Inalegwu ya yi wannan jawabi ne a Ranar Lahadi, 22 ga Watan Disamba, 2019. Inalegwu ya koka kan mummunar halin da Sharibu ta samu kanta a hannun ‘Yan ta’adda.

Wannan kungiya ta Dattawan Kiristoci ta na ganin cewa akwai rashin gaskiya tattare da sha’anin gwamnatin tarayyar, inda ta kuma nuna cewa mutanen kasar sun kauce hanya.

Bayan watsi da Ubangiji da ‘Yan kasar su ka yi, NOSCFE ta yi Allah-wadai da yadda harkar zabe ya ke kara lalacewa, inda rikicin zabe ya ke neman zama ruwan-dare a kasar.

Inalegwu ya jefi yankin Arewacin Najeriya da zargin cewa ba ayi wa Kiristoci adalci. A cewarsa ana hana yaran Kirista karatu a makarantun da ke Kebbi, Zamfara, da Katsina.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel