Obaseki: Oshimomhole ya sa aka amince da Shugabannin NDDC ba tare da fadawa Buhari ba

Obaseki: Oshimomhole ya sa aka amince da Shugabannin NDDC ba tare da fadawa Buhari ba

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya zargi Adams Oshiomhole da amfani da wasu manya a cikin fadar shugaban kasa, wajen samun damar kafa shugabannin NDDC.

Mista Godwin Obaseki ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya sa an amince da shugabannin hukumar ne ba da sanin shugaban kasa ba.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne ta bakin Kakakinsa, Crusoe Osagie, ya na mai cewa shugaban jam’iyyar ya yi wannan aiki ne lokacin da shugaba Buhari ba ya cikin kasar.

“Wani lamari da ya auku shi ne lokacin da Buhari ba ya Najeriya, Oshiomhole ya samu manyan jami’an fadar shugaban kasa su ka amince masa da shugabannin NDDC.”

KU KARANTA: Babban Sojan Najeriya ya yi maganar da ke tada hankali

Mai magana da yawun bakin gwamnan ya ke cewa Yaran Oshiomhole ne su ka cika wannan majalisa da aka kafa domin ta rika lura da duk ayyukan hukumar NDDC.

Mista Osagie ya ce hakan ya sabawa doka karara, sannan ya kara da: “Abin da ya ke so shi ne ya ci burinsa na kakaba wanda zai iya juyawa a matsayin gwamnan Edo”

A cewar gwamnan na jihar Edo, tsohon Mai gidan na sa, zai yi amfani da dukiyar kasa ta NNDC ne domin ya samu kudin da zai yaki gwamnatinsa a lokacin zaben jihar.

Yanzu haka dai an hurowa Adams Oshiomhole wuta ya sauka daga kujerar da ya ke kai a APC. Daga cikin masu wannan kira akwai bangaren APC na jiharsa ta Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel