Rikici da cacar baki ya kaure tsakanin manyan gwamnonin PDP guda 2

Rikici da cacar baki ya kaure tsakanin manyan gwamnonin PDP guda 2

Wani sabon rikici ya kaure tsakanin gwamnan jahar Ribas Nyesom Wike da gwamnan jahar Bayelsa Seriake Dickson, dukkaninsu yayan jam’iyyar PDP, inda kowannensu yake nuna ma takwaransa yatsa.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Gwamna Dickson yana gargadin Wike da hawainiyarsa ta kiyayi ramarsa, domin kuwa a cewarsa jahar Bayelsa ba wani bangare bane na jahar Ribas, don haka ya shiga taitayinsa.

KU KARANTA: Ganduje ya nada mace mukamin shugabar kafatanin ma’aikatan jahar Kano

“Ina so kowa ya sani wannan ne karo na farko da zan tanka ma Wike saboda irin yarintar da yake nunawa, na dade ina kawar da kaina daga gareshi da maganganun da yake furtawa da nufin cin mutuncin jaharmu da shuwagabanninta. Sanin kowa ne baya son jaharmu.” Inji shi.

Gwamnan na mayar da martani ne bisa wasu kalamai da Wike yayi a lokacin da Dickson ya kai ziyara ga wani babban basaraken jahar Ribas Amanyanabo of Kalabari Kingdom Theophilus Princewill kimanin watanni 8 da suka gabata.

A jawabinsa, Wike yace ziyarar da gwamnan ya kai jaharsa ya saba ma tsarin mulki, tunda dai bai sanar da hukumomin da suka dace ba, don haka ya zargeshi da kokarin kawo hargitsi da tarnaki jahar Ribas.

Don haka shi kuma Dickson ya mayar da martanin cewa babu wani gwamna a jahar Bayelsa dake bukatar amincewar Wike kafin ya kai ma wani ziyara a jahar Ribas, sa’annan ya yi alkawarin sake shiga Ribas a 2020 don bikin zagayowar ranar haihuwar Sarkin da zai cika shekaru 90.

Daga karshe gwamnan ya zargi Wike da hannu cikin kayen da PDP ta sha a zaben gwamnan jahar Bayelsa, haka zalika ya zarge shi kokarin raba kan jama’an kabilar Ijaw.

A wani labarin kuma, kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana ma magoya bayansa cewa ba su zabe shi domin ya dinga rikici da bangaren zartarwa ba, amma dole ne idan ta kama zasu iya samun sabani da juna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel