Ba’a zabe ni kaakakin majalisa don na yi rikici da Buhari ba – Gbajabiamila

Ba’a zabe ni kaakakin majalisa don na yi rikici da Buhari ba – Gbajabiamila

Kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana ma magoya bayansa cewa ba su zabe shi domin ya dinga rikici da bangaren zartarwa ba, amma dole ne idan ta kama zasu iya samun sabani da juna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gbajabiamila ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba a yayin taron karshen shekara inda yake raba ma jama’ansa alheri a jahar Legas, inda yace don kawai suna samun fahimtar juna da bangaren zartarwa hakan bai sa sun zama yan amshin shata ba.

KU KARANTA: Ganduje ya nada mace mukamin shugabar kafatanin ma’aikatan jahar Kano

Gbaja ya bayyana cewa matakin garkame iyakokin Najeriya na samar da kyakkyawar sakamako, kuma hakan ya tilasta ma yan Najeriya cin abincin da manoman gida suke nomawa, musamman ma shinkafa.

“Ina da tabbacin gwamnoni da dama suna samun arziki a wannan lokaci, idan kaga yadda yan Najeriya ke siyan shinkafar gida a wannan lokaci na kirismeti zaka tabbata manoma sun samu kudi, kuma da haka mun fara cin abinda muke nomawa.” Inji shi.

A yayin taron, Gbaja ya rabar da kyautar kudi ga mutane 500 domin kara musu karfin jari, ya rabar da motoci 23, kwamfutocin tafi da gidanka ga dalibai, janareta da sauran kayayyaki da dama. “Fatana shi ne da zarar mun gama shekaru hudunmu Surulere za ta canza.”

A wani labarin kuma, Wani sabon rikici ya kaure tsakanin gwamnan jahar Ribas Nyesom Wike da gwamnan jahar Bayelsa Seriake Dickson, dukkaninsu yayan jam’iyyar PDP, inda kowannensu yake nuna ma takwaransa yatsa.

Majiyarmu ta ruwaito Gwamna Dickson yana gargadin Wike da hawainiyarsa ta kiyayi ramarsa, domin kuwa a cewarsa jahar Bayelsa ba wani bangare bane na jahar Ribas, don haka ya shiga taitayinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel