NUEE: Ma’aikatan wutar lantarki sun fara barazanar shiga sabon yajin aiki

NUEE: Ma’aikatan wutar lantarki sun fara barazanar shiga sabon yajin aiki

Akwai yiwuwar duhu ya karade Najeriya nan gaba, inda mu ka samu labarin cewa kungiyar NUEE ta Ma’aikatan wutan lantarkin kasar nan su na barazanar shiga yajin aiki.

‘Ya ‘yan wannan kungiya sun fara nuna cewa za su iya cigaba da yajin aikin da su ka fara kwanaki. Dama can an dakatar da yajin ne domin gwamnati ta saurare kukansu.

A Ranar 23 ga Disamban 2019, mu ka samu rahoto cewa idan har gwamnatin Najeriya ta gaza cika alkawuran da aka yi da ita, Ma’aikatan wutar lantarkin za su koma yajin aikin.

Wannan kungiya ta na kukan cewa hukumar BPE ta ki biyan sama da tsofaffin Ma’aikatan wuta 2, 000 da aka sallama daga kamfanin PHCN aiki kudinsu, tun cikin shekarar 2013.

Haka zalika wannan kungiya ta na korafin cewa hukumar BPE ta Najeriya ta karbe makarantun da ta gina, ta mikawa wadanda su ka zuba kudinsu a kamfanonin wutan kasar.

KU KARANTA: Minista ya fadi dalilin shirin kara kudin shan wutar lantarki

NUEE ta bayyana cewa ba a bi doka wajen karbe masu makarantun na su ba. Sannan ana karar cewa ba a biya wasu tsofaffin ma’aikatan wutan cikon kudin aikinsu ba.

Ma’aikatan da su ka yi aiki da kamfanin wutar lantarkin Najeriya na PHCN fiye da 50, 000 ne su ke bin bashin kudin sallama a dalilin rashin biyansu cikakken hakkinsu.

Sakataren kungiyar NUEE, Kwamred Joe Ajaero ya tabbatar da cewa dole a cika yarjejeniyar da ta sa su ka janye yajin aikinsu tun farko, idan ba a so a koma gidan jiya.

Ajaero ya ce NUEE ta na zura idanu domin ganin gwamnati ta cika alkawuran da ta dauka. Sai dai wata takwarar kungiyar mai suna SSAEAC, ta fito ta na kishiyantar ta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel