Mayakan Boko Haram sun kai hari a kan ma'aikatan 'jin kai', sun kashe 3 tare da raunata 2

Mayakan Boko Haram sun kai hari a kan ma'aikatan 'jin kai', sun kashe 3 tare da raunata 2

A ranar Lahadi ne mutane uku suka rasa rayukansu bayan harin da ake zargin wasu 'yan Boko Haram sun kai wa ma'aikatan 'jin kai' a jihar Borno. Wasu mutane biyu daban kuwa an yi garkuwa dasu, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

Mayakan sun kai harin ne a kan titin Maiduguri zuwa Monguno.

Majiya mai karfi daga ofishin majalisar dinkin duniya dake Maiduguri a jihar Borno, ta tabbatar da harin. Duk da dai, ko a halin yanzu babu gamsassun bayanai a kai. Don jami'an ofishin majalisar dinkin duniyar sun tabbatar da cewa yayi wuri da su fitar da bayanai.

Wata majiya daga ofishin ta tabbatar da cewa, duk wadanda aka yi garkuwa dasu din mata ne.

DUBA WANNAN: Gaskiyar abun da yasa na ajiye mukamin da Matawalle ya nada ni - Marafa

"Zan iya tabbatar muku da cewa, mummunan lamarin ya faru ne a kan titin Monguno amma ba za a iya cewa mutane nawa bane abun ya ritsa dasu ba," in ji majiyar da ta bukaci a boyeta.

Premium Times ta gano cewa, ma'aikatan jin kai da aka hara na wata kungiya ne da ake kira da Alima.

Alima kungiyar jin kai ce ta farko da ta fara zuwa garin Monguno a watan Yuni 2016. Har yanzu kungiyar tana taimako a Monguno a jihar Borno.

Duk wani yunkurin tuntubar jami'an Alima don jin bayani dalla-dalla, ba a samu nasara ba a lokacin rubuta wannan rahoto.

Rundunar soji a halin yanzu suma ba a samesu ba don tabbatar da aukuwar lamarin. Hakazalika, basu saka wata takarda ko sanarwa ba a dangane da harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel