Gaskiyar abun da yasa na ajiye mukamin da Matawalle ya nada ni - Marafa

Gaskiyar abun da yasa na ajiye mukamin da Matawalle ya nada ni - Marafa

- A ranar Asabar ne rahotanni suka bayyana cewa an fara samun baraka a sabuwar gwamnatin jihar Zamfara

- Hakan ya biyo bayan murabus din da wani kwamishina da mai bawa gwamnan jihar shawara suka yi da rana tsaka

- Daya daga cikin wadanda suka yi murabus din, Alhaji Sambo, kani wurin tsohon Sanata Kabiru Marafa, ya bayyana dalilinsa na fice wa daga gwamnatin Matawalle

Alhaji Sambo, kani wurin tsohon sanatan jihar Zamfara, Kabiry Marafa, ya yi bayani dalla - dalla a kan dalilinsa na ajiye mukamin mai bayar da shawara da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya nada shi tare da bayyana cewa babu wata baraka, ko kadan, a tsakaninsu.

A cikin wani jawabi mai dauke da sa hannunsa da aka raba wa manema labarai, Sambo ya bayyana cewa ya ajiye mukamin ne domin ya samu sukuni da sararin mayar da hankali a kan kasuwancinsa da kuma bawa wasu dama domin a dama da su a gwamnatin da suka bawa gudunmawa wajen kafuwarta.

Sambo, wanda tsohon mamba ne a majalisar dokokin jihar Zamfara daga shekarar 1999 zuwa 2003, ya ce babu wata baraka a tsakaninsa ko yayansa da gwamna Matawalle tare da kara bayyana cewa har yanzu zasu cigaba da mu'amala tare domin ciyar da jihar Zamafara gaba.

Tsohon mai bawa gwamnan shawara ya ce Matawalle tamkar yayane a wurinsa saboda kyakyawar alakar dake tsakaninsa da yayansa, Sanata Marafa.

Kazalika, ya bayyana cewa ya sanar da Sanata Marafa kafin ya mika takardarsa ta yin murabus ga gwamna Matawalle.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel