CBN ya soke karbar N52.5, N65. wajen aike ta yanar gizo da aiki da ATM

CBN ya soke karbar N52.5, N65. wajen aike ta yanar gizo da aiki da ATM

Babban bankin Najeriya na CBN ya dauki mataki game da cire kudi da ake yi idan aka yi amfani da na’urar ATM ko kuma aka yi aiken kudi.

Haka zalika an yi garambawul ga tsarin karbar wasu kudi lokaci bayan lokaci da sunan ana duba katin mutum na ATM. Bankin ya fadi wannan dazu.

A wani jawabi da babban bankin kasar ya fitar ga sauran bankuna da hukumomin kudi mu ka samu wannan labari a Ranar 22 ga Watan Disamba.

Za a rika karbar N10 ne ga wanda ya yi aiken kudin da ba su haura N5000 ba. Haka kuma za a cire N25 ga wanda ya aika abin da ya kai N50, 000.

A baya an kasance bankuna su kan zare N50 ga wanda ya aika kudin da bai gaza N500, 000. Yanzu wannan sabon tsari da aka fitar ya kawo sauyi.

KU KARANTA: Ta tabbata za a kara kudin wuta a Najeriya a nan gaba

A sabuwar dokar da aka kawo, za a rika karbar N35 ne kacal idan mutum ya yi amfani da na’urar ATM din da ba na bankin da ya ke adana kudinsa ba.

Bayan wannan, CBN sun cire kudin da aka saba karba wajen adana katin ATM ga masu karbar albashi ta banki inji Darektan yada labarai na bankin.

Ga masu adana kudi, an rage abin da ake karba a kan katin ATM daga N50 a duk wata, zuwa N50 a cikin watanni uku. An samu ragin N400 a shekara.

Gwamnati ta hannun CBN ta tsananta matakai ga bankunan da aka samu su na saba doka. Za a rika karbar tarar N2, 000, 000 ga wanda ya yi laifi.

Isaac Okorafor shi ne ya bayyana duk wannan. Da alamun cewa daga Junairun 2020, za a daina karbar kudi wajen sake bude akawun din da aka rufe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel