Wutan lantarki: Karin farashi ya zama dole a Najeriya Inji Minista

Wutan lantarki: Karin farashi ya zama dole a Najeriya Inji Minista

Bisa dukkan alamu nan da wasu kwanaki kadan ‘Yan Najeriya za su fara biyan farashin da ya zarce abin da su ka saba biya domin samun hasken wutar lantarki a kasa.

Gwamnatin tarayya ta na shirin kara farashin wuta a Najeriya da zarar ta kammala ayyukan da ake yi a fadin kasar inji Ministan harkar lantarki watau Injiniya Sale Mamman.

Ministan ya bayyana cewa za a dada farashin shan wutan ne bayan an samu kari a kan yadda ake samar da wutar lantarki har ya zo ga kamfanonin da ke da alhakin rabo.

Sale Mamman ya nuna cewa farashin da ake shan wuta a kasar ya jawo cibaya a game da samar da lantarki zuwa ga masu bukata. Wannan ya sa dole za a kara farashin wutan.

KU KARANTA: Hoton cikin gidan Attajirin Afrika Aliko Dangote

Wutan lantarki: Karin farashi ya zama dole a Najeriya Inji Minista

Minista Saleh Mamman ya ce kudin wuta zai karu a Najeriya
Source: Facebook

Mai girma Ministan ya yi alkawari cewa za a cigaba a sha’anin wutar lantarki da zarar gwamnatin tarayya ta kammala ayyukan wutan da ta ke yi a tasoshin da ke Najeriya.

“Ayyukan da ake yi za su kara karfin wuta a Najeriya. Idan wuta ta gyaru, dole a kara farashi a fadin kasar, saboda dole a maida kudin da ake kashewa wajen samar da wutan”

Injiniya Mamman ya shawarci ‘Yan Najeriya da su rika biyan kudin wutansu, tare da fadawa jama’a cewa gwamnati ta na daukar matakai na ganin lantarki ya inganta.

The Nation ta rahoto Ministan ya na wannan jawabi a Ranar 21 ga Watan Disamban 2019. Har yanzu dai wuta ya na cikin abin da ke ci wa ‘Yan Najeriya tuwo a kwarya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel