Majalisar Dattawa ta zama sai yadda Shugaban kasa ya ce bayan tafiyar Saraki

Majalisar Dattawa ta zama sai yadda Shugaban kasa ya ce bayan tafiyar Saraki

Tun da aka kafa majalisa ta tara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama ya na samun duk abin da ya bukata daga hannun ‘Yan majalisa wanda Sanata Ahmad Lawan ya ke jagorantarsu.

Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta fito da shi a yau Ranar Lahadi, 22 ga Watan Disamban 2019, ya nuna cewa babu wani kalubale da fadar shugaban kasa ta ke samu a wannan majalisar.

Kyakkyawar alakar da ke tsakanin shugabannin majalisar da shugaban kasa ya sa aka amince da kasafin kudin cikin ruwan sanyi, haka duk mukaman da aka nada su kan samu shiga sumul.

A majalisar baya wanda Bukola Saraki ya jagoranta, ba kowane kokon-barar shugaban kasar ba ne ya ke samun karbuwa. Sanatoci su kan yi nazari kafin su amince da bukatun shugaba Buhari.

Bayan zuwan Lawan, jama’a sun fara yi wa Majalisar tarayya kallon ‘Yan amshin Shata, ganin yadda aka fara da tantance wadanda shugaban kasar ya zaba a matsayin Minista a majalisa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana wata matsala guda da ke fuskantar mulkinsa

Majalisar Dattawa ta zama sai yadda Shugaban kasa ya ce bayan tafiyar Saraki

Ana ganin fadar shugaban kasa ta na juya Majalisar Dattawa
Source: UGC

Ban da tantance Ministoci da sauran wadanda nadin mukamansu zai bi ta gaban Sanatoci, majalisa ta kan yi gaggawar amincewa da duk wani kudiri da ya fito daga teburin shugaban kasa.

A cikin kwana 5 ne kacal Sanatoci su ka amince da Ministoci 43 da Buhari ya turo masu. A lokuta da-dama a kan cewa zababbun Ministocin ne su duka su wuce kurum ba tare da ko tambaya ba.

A irin haka ne aka tantance shugabannin hukumomin NDDC da NAHCON. Sai dai wani daga cikin wanda aka zaba a hukumar INEC ya samu cikas a majalisa har ta kai aka ki tantancesa kwanaki.

Wannan zargi na ‘Amshin-Shata’ ya na kan har Sanatocin hamayya wanda su ke yin gum a majalisa. Ana zargin cewa ba su mukamai masu tsoka da aka yi ne, ya sa ba su iya cewa komai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel