Majalisa: Adeyemi ya zama Shugaban Kwamitin harkokin jiragen sama

Majalisa: Adeyemi ya zama Shugaban Kwamitin harkokin jiragen sama

A karshen makon nan ne Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma yanzu a majalisar dattawa, Smart Adeyemi, ya zama shugaban kwamitin sufurin jirgin sama.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, shi ne ya sanar da nadin Smart Adeyemi a matsayin shugaban wannan kwamiti Ranar Juma’a.

A Ranar 20 ga Watan Disamban 2019 da aka yi zaman karshe a majalisa, Smart Adeyemi ya dare kan wannan kujera wanda a baya Dino Melaye ya ke rike da ita.

Ahmad Ibrahim Lawan ya sanar da wannan sauyi da aka yi ne a zauren majalisar. Bayan wannan sanarwa aka dage zaman majalisa sai Ranar 28 ga Watan Junairu.

KU KARANTA: Zaben Dino Melaye ya na cikin wanda ya ba Najeriya mamaki

Majalisa: Adeyemi ya zama Shugaban Kwamitin harkokin jiragen sama

Ahmad Lawan ya ba Sanata Adeyemi rikon kwamiti a Majalisar Dattawa
Source: Facebook

A Ranar 30 ga Watan Nuwambam Sanata Smart Adeyemi ya dawo majalisar dattawan kasar. Wannan ne karonsa na uku a matsayin Sanatan Kogi ta Yamma.

Idan ba ku manta ba kotun sauraron karar zaben jihar Kogi Kogi, da kuma na daukaka kara, sun ruguza zaben da ya ba Dino Melaye da PDP nasara a Watan Maris.

Wannan ya sa INEC mai zaman kanta ta shirya zabe a Ranar 16 ga Watan Nuwamba. Wannan zabe ya kai wa hukumar dare, amma a karshe APC ta yi nasara.

Bayan darewa kan kujerar da Dino Melaye ya kasance a kai tun 2015, Adeyemi ya gaje kujerar kwamitin tsohon Sanatan na PDP wanda ya na cikin masu tsoka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel