ASAW: Mutumin Ibo ya kamata ya gaji Buhari a Shugaban kasa a Najeriya

ASAW: Mutumin Ibo ya kamata ya gaji Buhari a Shugaban kasa a Najeriya

Wata kungiya mai suna Anambra State Association Worldwide wanda aka fi sani da ASAW, ta roki mutanen Najeriya su ba Ibo damar mulkin Najeriya na tsawon wa’adi biyu a zaben 2023.

Wannan kungiya ta ASAW ta yi kira ga ‘Yan kasar su marawa Ibo baya su yi shekaru takwas a jere su na mulki, domin ganin kowane bangare ya samu damarsa, Daily Trust ta rahoto wannan.

Kamar yadda mu ka samu labari, kungiyar ta mutanen Yankin Anambra ta nuna cewa adalci da gaskiya da bin doka shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mikawa Ibo mulki a 2023.

Kungiyar ta bakin shugabanta na kasa, Dr. Nwachukwu Anakwenze, ta ce mutanenta na Ibo sun shirya tsaf ta kowane bangare domin ganin sun karbi ragamar mulkin Najeriya a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Wasu daga cikin sakamakon zaben da su ka fi ba kowa mamaki a 2019

Nwachukwu Anakwenze ya yi wannan jawabi ne jin kadan bayan kungiyarsa ta dauki nauyin kula da wasu marasa lafiya mutum 500. Kungiyar ta dauki dawainiyar Bayin Allah kyauta.

An yi wannan aiki ne a Garin Abbagana da ke cikin karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra. Anakwenze yace abin da ya fi dacewa da kasar nan shi ne fafutukar ganin Ibo ya karbi mulki.

Shugaban kungyar ya yi kira ga mutane su dage da kokarin ganin Inyamuri ya gaji gwamnatin Buhari, tare da kira ga sauran masu neman takara a 2023 duk su hakura su janyewa Inyamurai.

Mun fahimci cewa har Nwachukwu Anakwenze ya kammala jawabinsa a madadin kuniyar ASAW, bai bayyana jam’iyyar da za ta tsaida Ibo a matsayin ‘dan takarar na ta a zaben 2023 ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Online view pixel