Rashin samun aikin yin ‘Yan Makaranta ya na da ban takaici – Buhari

Rashin samun aikin yin ‘Yan Makaranta ya na da ban takaici – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga jami’o’in Najeriya su kara kaimi wajen kokarin ganin cewa wadanda su ka kammala karatu su na samun abin yi a fadin kasar nan.

Ana kukan cewa Matasa da-dama ba su cancanci a ba su aiki ba. Muhammadu Buhari ya nuna cewa wannan matsalar rashin samun abin yi, abin damuwa ne ga gwamnatin ta sa.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a wajen taron yaye ‘Daliban jami’ar tarayya ta fasaha da ke Garin Akure a jihar Ondo. An yi wannan biki ne a jiya, Asabar 21 ga Watan Disamba, 2019.

Shugaban na Najeriya ya samu wakilcin Mataimakin Sakataren hukumar NUC mai kula da jami’o’in gwamnati ne a taron. Dr. Suleiman Yusuf ne ya wakilci shugaban kasar jiya.

A cewarsa, wannan gwamnati mai-ci ta na ganin ilmi shi ne tubulin duk wani cigaban kasa, yayin da jami’o’i su ke kololuwar wajen karatu domin nan ne gidajen yada ilmi.

KU KARANTA: Ana so a kafa sabuwar Jami'ar Tarayya a Garin Katsina

“A Duniyar yau da aka cigaba, inda ilmi ya zama kudi, dukiyar kasa da muhimmancin ta a Duniya ya danganta da karfin ilminta, abin da na ke sa rai shi ne jami’o’inmu za su dage…

…Za su sauke nauyin da ke kansu na koyarwa da bincike da nazari wajen ganin Najeriya ta shiga cikin sahun da za a rika nuni da ita a cikin sauran kasashen Duniya. Inji Buhari.

“A game da wannan, gwamnati ta na sa rai jami’o’i su rika yaye ‘Dalibai da su ke da ilmin da ake bukata da kuma sanin aiki, da dabi’ar kirki da kwarewan da su kawo cigaban kasa.”

Shugaban kasar ta bakin Suleiman Yusuf, ya ce ya na tsammani jami’o’i za su maida hankali wajen yaye ‘Daliban da za su rika samun aiki ba wadanda za a rasa inda za a kai su ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel