Me ya yi zafi? Babban dan sanda ya harbe dan uwan aikinsa, ya kashe kansa a take

Me ya yi zafi? Babban dan sanda ya harbe dan uwan aikinsa, ya kashe kansa a take

Tashin hankali da alhini ya samu jama'a a yankin Dutse na babban birnin tarayyar Abuja. A yau Asabar ne Sifetan 'yan sanda, John Markus, ya kashe wani abokin aikinsa sannan daga baya ya kashe kansa.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar a hedkwatar 'yan sanda dake Dutse dake Abuja. Sifetan 'yan sandan ya raunata wani dan sandan daban bayan wanda ya kashe.

Kwamishinan 'yan sandan babban birnin tarayyar, Bala Ciroma, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin din Channels, ta tattaunawar wayar da suka yi.

Lamarin ya faru ne bayan da Markus ke kan aikinsa a safiyar yau. Ya harba jerin harsasai cikin iska.

DUBA WANNAN: Yadda gobara ta lashe matan aure biyu da yara biyar a Katsina

An gano cewa, Kofur Mathew Akubo ya jawo hankalinsa da ya daina harbin nan. Amma sai sifetan 'yan sandan ya juya tare da harbe abokin aikin nashi. A take kuwa ya fadi matacce.

Bayan nan, SP Abdullahi Ovanu ya fito daga ofishinsa don duba abinda ke faruwa amma sai Sifetan sai ya harbesa a kafada.

Bayan mintoci kadan da aukuwar lamarin, Markus ya kashe kansa ta hanyar harbin kansa da bindiga ta bakinsa.

Gawar kofur din da sifetan 'yan sandan suna adane a wajen adanar gawawwaki dake babban asibitin Kubwa. SP Abdullahi kuwa yana asibiti inda yake samun kulawar masana kiwon lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel