Ganduje ya yi wa manyan sakatarorin gwamnatinsa canjin wuraren aiki

Ganduje ya yi wa manyan sakatarorin gwamnatinsa canjin wuraren aiki

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da canje-canjen ma'aikatu ga manyan sakatarorin gwamnatinsa don samun aiki nagari a ma'aikatun jihar. Wannan na kunshe ne a takardar da Abba Anwar, babban sakataren yada labarai na Ganduje, ya fitar a ranar Asabar.

Ya ce, Lawan Ahmed daga ma'aikatar kasuwanci ya koma ofishin shugaban ma'aikata, Saleh Ado Minjibir daga gidan gwamnati zuwa ma'aikatar kananan hukumomi, sai kuma Dr Binta Umar Bala daga ma'aikatar ilimi zuwa ma'aikatar lafiya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Sauran sun hada da Abba Kailani daga ma'aikatar kananan hukumomi, Abba Ibrahim Wada zuwa gidan gwamnatin jihar, Amina Aminu Kano daga hukumar fansho zuwa ma'aikatar ruwa da kuma Usman Bala Muhammad, daga ma'aikatar lafiya zuwa ma'aikatar yada labarai.

Sauran wadanda abun ya shafa sun hada da Zakari Sadiq Buda daga ma'aikatar kudi zuwa ma'aikatar al'adu da shakatawa, Binta Salihu daga SERVICOM zuwa al'amuran shugabanci, Ahmed Salisu Abba, daraktan kasafin kudi zuwa babban sakataren ma'aikatar aiyuka da habaka abubuwan more rayuwa..

DUBA WANNAN: Kallabi tsakanin rawuna: Ganduje ya nada mace a matsayin shugabar ma'aikatan jiha

Akwai Adamu Abdu Faragai, daga ma'aikatar aiyuka na musamman zuwa ma'aikatar aikin gona, Dr Zainab Braji daga al'amuran shugabanci zuwa ma'aikatar filaye sai kuma Hussaini Umar, daga daraktan kananan hukumomi zuwa babban sakataren ma'aikatar aiyuka na musamman.

Akwai Lawan Shehu da aka mayar ma'aikatar kudi, Dahiru Ada'u daga ma'aikatar aiyuka da habaka ababen more rayuwa zuwa ma'aikatar ilimi, Hadi Bala daga ma'aikatar aiyukan gona zuwa sakataren gidan gwamnati.

Hakazalika, Auwalu Ilyasu Riruwai ya bar ma'aikatar ruwa zuwa hukumar fansho, Tijjani Bello Abubakar daga ma'aikatar filaye zuwa SERVICOM sai kuma Hafsatu Ilyasu Aliyu, daga ma'aikatar yada labarai zuwa ma'aikatar harkokin addini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel