Buhari ya halarci taron ECOWAS da takwarorinsa (Hotuna)

Buhari ya halarci taron ECOWAS da takwarorinsa (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron Gamayyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma karo na 56 dake gudana ranar Asabar, 21 ga watan Disamba, 2019 a hedkwatar ECOWAS dake unguwar Asokoro, birnin tarayya Abuja.

Buhari ya karbi bakuncin takwarorinsa na kasashen yankin irinsu Nijar, Ghana, da sauransu.

Shugaba Buhari ya jagoranci shirin inda ya fara da mika sakon ta'aziyya ga gwamnatin Nijar kan rashin Sojoji 73 da yan Boko Haram suka kashe a makon baya.

Shugabannin kasashen sun tattauna kan lamarin tsaron yankin, amfani da samfurin kudi iri daya da kuma zaben shugaban kasar Guinea Bissau.

Daga cikin wadannan suka halarci taron sune shugaban bankin cigabar Afrika, Akinwumi Adesina; wakilin shugaban majalisar dinkin duniya, Mohammed Ibn Chambas; shugaban kungiyar ECOWAS, Jean Claude Brou.

Sauran sune shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou; shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe; shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Kabore; shugaban kasar Guinea Conakry, Alpha Conde da shugaban kasar Gambia, Adama Barrow.

Buhari ya halarci taron ECOWAS da takwarorinsa (Hotuna)

Buhari ya halarci taron ECOWAS da takwarorinsa (Hotuna)
Source: Depositphotos

Buhari ya halarci taron ECOWAS da takwarorinsa (Hotuna)

Buhari ya halarci taron ECOWAS da takwarorinsa (Hotuna)
Source: Facebook

Source: Twitter

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel